⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 50: Chapter 50

Amira na tsaye a jikin windownta har Ahmad ya ja motarsa ya bar gidan, kwana biyu ta huta da leƙe leƙe amma yau tunda suka dawo duk wani ƙanƙantar motsi so take ayi akan idanunta, she was shocked to bone marrow da taga Ahmad ya kawo Saif gidan kuma amma wai ba wajenta ba wajen wata wai Na’ima, kuma shima Saif ɗin bata ga alamar ya nuna yana son zuwa ƙofarta ba ita mamarsa kamar ma bai san gidansu Mummynsa aka kawo sa ba, he followed babanshi straight to part ɗin Na’ima, wani irin tafasa kawai take yi zuciyarta na bugawa, sai yanzu da ta ga Saif taga ma bazata iya ba ita kawai a bata ɗanta.

Kamar mahaukaciya ta nufi kan gadonta ta figi gyalenta da wayarta ta nufi ƙofa ta shiga sauƙowa a zafafe zata je ta sami Na’ima ta bata ɗanta, tana shirin buɗe ƙofar palour ta fita wayar hannunta ya kama ruri, ta fito ta janyo ƙofar tare da ɗaga kiran ta kai kunnenta, yadda taji muryar Nuwaira cike da annashuwa ya sa ta dakata daga bakin palournta tace

“Nuwa me ya faru?”

“Ke nayi aureeeee!!” Ta faɗa da ƙarfi cike da murna, Amira ta dafe ƙirji tace

“bari wasa” wani tsaki ta ja tace

“Wallahil azeem yanzu aka ɗaura aurena da mutuminki, ya nuna min hau na nuna masa na fisa iya shi in dai hau ne, na kai aka saka mini shi a kaca, ai yanzu wallahi mai rabani da shi kuma sai mahaliccinmu, matarsa da yarsa da shi kuwa sai gani sai hange” Amira da tuni sai murna take na auren da Nuwaira tayi tace

“Am very happy for u babe, yanzu ne zaki yi asalin rayuwa mai yanci Nuwa, ki zage ki more kuma a halal ɗinki”

“Ke dai bari, faɗa ma ai ɓata baki ne ƙawata, ke wato ko tausayin ahalinsa baki ji ba” Amira ta ƙyalƙyale da dariya tace

“Ai su kam sai dai su rungumi sorry! Kaya sun iso hannun mai shi, Allah ya basu dangana” nuwaira ta tuntsure da dariya tace

“Shiyaasa nake ƙaunarki Ameerata” sai a lokacin Amira ta tuna dalilin fitowarta, ta kalli ƙofar Na’ima tare da faɗin

“Kinsan me yake faruwa a gidannan yanxu wai?” Daga ɗaya ɓangaren Nuwaira tace

“what happened?”

“Saif Albi ya kawo gidannan” cike da confusion Nuwaira tace

“and so? Ba abinda kike so ba kenan ya dawo miki da ɗanki? Ko da gaske wai kin bar musu ɗinne?”

“Su sun ma isa in bar musu? Nuwa ba wajena ya kawo shi wajen Na’ima ya kawo Saif, yanzu haka Saif yana ƙofarta” Nuwaira tace

“What!? Ban gane ba wata Na’imar yaushe ta dawo gidan?” Kallon compound ɗin kawai Amira take yi cike da zafin zuciya tace

“Yau suka dawo Nuwa, mummy ta cuce ni, ashe bai sake ta ba ashe suna tare Nuwa, shima kwanansa biyu baya gidannan yana can tare da ita sai gashi yau sun dawo tare kinga kenan ai aiki ya lalace, da nayi magana yace wai ai kwananta ne, shine kuma yanzu ya tafi ya ɗauko mata Saif ya kawo mata, ɗana!, ɗana fa Nuwaira” tana faɗa ta fashe da kuka, Nuwaira ta lailayo wani hamshaƙin ashar ta dire tana faɗin

“Shine kike musu kuka dan iskanci? Kukan uwar me kike?” Amira ta share idanunta tace

“Na gaji Nuwa, babu abinda nake tsinta a gidannan yanzu sai takaici, jiya sai da nayi wa kaina overdose ɗin maganin ƙwaya na iya bacci, damuwa ya min yawa Nuwa, ni ya zanyi?”

“Hehe, yanzu kina ina?” Nuwaira ta faɗa cike da bala’i

“Gani na fito zan je in ce mata ta bani ɗana tunda ba ita ta haifa min shi ba”

“Kar ki je jirani ina zuwa yanzu, ya kamata ki ci kutumar uban Na’imar nan da tushe”

“Toh” Amira ta faɗa tana share hawaye

“Ki koma ki jira ni! Ki bani minti 10, yanzu haka na ɗauko makulli zan taho gidannaki yanzu, ina ogannaku dai baya nan?”

“Baya nan ya koma office”

“To gani nan zuwa” tana gama faɗin haka ta katse wayar, Amira ta juya ta danna bell Mary ta buɗe mata ta koma cikin palourn ta zauna a kujera ta kwantar da kanta a hankali hawaye na cigaba da sintiri a fuskarta.

Mary dai kallonta kawai take kafin ta wuce ɗaki a hankali jikinta duk a sanyaye ganin uwar ɗakinta na kuka.

Kusan minti sha biyar aka danna bell ɗin again, Amira ta tashi da sauri ta nufi ƙofa ta buɗe, Nuwaira da ke tsaye a bakin ƙofa bata ma shigo ba tace

“Fito muje” Amira ta saka takalmanta ta fito tana share idanunta tana faɗin

“Sabon mijinnaki kuma ya barki kika fito” tsaki Nuwaira ta ja tana faɗin

“Rabu da wannan dan Allah shi ya ma isa ya ce min ga inda zani da inda bazani ba ai tun can ba haka muka faro da shi ba, yanzu kuwa da ya zama mijina ai sai abinda ya gani” Amira ta kalleta da ɗan kumburarrun idanunta suna tafiya towards part ɗin Na’ima tace

“A hoton da kika nuna min shi kuwa kamar zai yi bala’i”

“Sai dai yayi ma kansa bala’i ba dai ni Nuwa ba, ke bare yanzu fa ce miki nayi an saka shi a kaca, 5M da kika bani fa duka kaiwa nayi aka min yadda za’a yi da shi kinsan aiki nawa ne a kansa? kin taɓa ganin wanda ke kaca yana bala’i? Ai sai dai bin umarni”

Amira ta gyaɗa kai “hakane, ashe abinda kike shiryawa kenan shiyasa kika zubar da cikin”

“Bazan iya da wahala bane, ciki ko jidali, shiyasa kema na rabaki da wani ciki wallahi ai kinsan wahalar da kika sha akan Saif” dai dai lokacin suka iso part ɗin Na’ima suka ɗan haura small stairs ɗin zuwa front door, Nuwaira ta kalli Amira tace

“Saura idan mun shiga kiyi mata sanya kinji tunda ke baki da wayo da hankali”

“Hmm” kawai Amira tace tana kai hannu ta danna bell ɗin, Nuwaira kuwa sai jijjiga ƙafa take yi.

Na’ima da Saif da ke cin noodles suka ɗaga kai suka kalli ƙofar, tace masa

“Ko papa ne ya dawo?” Gyaɗa mata kai yayi yana kai small fork ɗin hannunsa bakinsa yace

“Maybe” ta ajiye plate ɗinta tare da miƙewa tana gyara zaman shirt ɗin jikinta, dan shirt ce fara a jikinta mai buttons da blue jeans sai hula dake kanta, ta ƙarasa ta buɗe ƙofar fuskarta ɗauke da fara’a.

Ganin waɗanda ke bakin ƙofar tuni murmushin da ke kwance a fuskarta ya fara raguwa dan ita Amira ma kaɗai ta sani bata san wannan babbar matar dake gefen Amirar ba, fuskarsu kaɗai ta kalla ta san ba alkhairi a tattare da su, ta ɗan ja ta tsaya tana kallonsu tace

“Sannu da zuwa” directing maganartata to Amira, Nuwaira ce ta fara bangaje Na’ima ta shiga ɗakin kafin Amira ma da ta haɗe rai fuskarta babu alamun annuri ko ɗigo ta bi bayan Nuwaira har cikin palourn suka barta tsaye bakin ƙofa, ta juya ta bi su da kallo cike da mamaki, ƙin rufe ƙofar tayi ta barsa a wangale ta shigo cikin palourn itama tana ɗan haɗe nata ran dan bata ga alamar da mutunci suka zo ba ta ɗan gyara hularta tare da tsayawa gefen kujera tana kallonsu tace

“How may i help u?” Amira dai kallon Saif kawai take yi da ke zaune kan carpet yana cin noodles, kafin ta bi gidan da kallo, komai na gidan ba wanda ta zo ta samu rannan bane like every single thing is changed, Nuwaira ma sosai part ɗin ya mata kyau, plus ita dama bata taɓa haɗuwa da Na’ima ba, bata san haka yarinyar take ba gata dai ƙarama amma sai shegen kyau yanxu ta gano dalilin Ahmad na maƙale mata kuturu, ita dai Na’ima na ta tsaye tana kallonsu tana jiran ganin abinda suke shirin yi, so take ma ta ƙarasa ta ɗauko wayarta dake gefen Saif ta kira Ahmad, cause there’s no way they’ll come into her house kalan haka ita kam bata so.

Nuwaira da takaici ya isheta ganin Saif ya kallesu yace “mummy” amma kuma bai taso yaje wajenta ba sai ma cin noodles ɗinsa kawai da yake yi yana kallonsu yasa ta ƙarasa ta karɓe bowl ɗin noodles ɗin tayi cilli dashi tare da faɗin

“Tashi ka wuce mu tafi dan ubanka ɗan gidan kishiya mara kishin uwarsa”

tuni Saif ya fashe da kuka, dan dama ganin Nuwaira kusa da mummynshi ya sa ya ƙi zuwa, jininsu sam bai haɗu ba.

Dukansu ba wanda ya kula Na’ima, Amira ma ta ƙarasa tana karɓar hannun Saif a na Nuwaira da ta kama shi tana ƙoƙarin miƙar da shi amma yana kuka yana lanƙwashe ƙafafunsa alamun ba zai taka ƙasa ba, Amira ta kama hannunsa tace

“Saif!!!!” Tsayawa yayi yana kallonta, tace

“Wuce mu tafi gida!” Ya maƙale mata kafaɗa tare da kallon Na’ima da ke tsaye still tana kallonsu bayan ta gama kallon noodles ɗin da Nuwaira ta ɓarar mata a palour, tausan zuciyarta kawai take yi tana Allah Allah su ɗauki yaron su tafi ta rufe ƙofarta.

Ganin Saif na kallonta ta ɗan masa murmushi tace

“Go with ur mom champ” ai kuwa kamar jira dama Amira take ta sake hannun Saif ta juyo tana kallon Na’ima tace

“Ke dan uwarki da ubanki ke zaki faɗa ma ɗana ya bini ko kar ya bini, sanda na tsuguna na haife sa kina ina? Kinsan Allah ki shiga taitayinki dani” kallonta kawai Na’ima keyi baki sake, cause bata ga wanann zagin coming ba, full of innocence tace

“Don’t say that to me again, keep my parents out of this” Nuwaira tayi wani shewa tana faɗin

“Au kishiyar taki bata iya hausa ba ashe”

“Dan uwatta kar taji” rungume hannunta a ƙirji Na’ima tayi tana kallonsu kawai, Nuwaira ta mata wani banzan kallon tace

“Matsiyaciya, u’re shameless wallahi, banda ma jaka ki aurar mata miji kina kwana da shi sannan kice zaki karɓe mata ɗa shegiya karuwa” Saif kawai Na’ima ta koma take kallo, da shima yayi shiru yana kallonsu.

Ganin ba kulasu Na’imar zatayi ba Amira tace “ Nuwaira ke kika tsaya ma kike faɗa tana faɗa, ai ba laifinta bane uwarta da ta haifeta ta raineta ce ta koya mata, like mother like daughter, dukansu are filthy” idanun Na’ima har ya fara kaɗawa yana tara ruwa amma ta gagara cewa komai, Nuwaira ta fara tafa hannuwanta da ƙarfi a kusa da fuskar Na’ima tana faɗin

“Mayya! Mayya! Idan ma baki ji wannan ba to Witch! Ure a witch” sai a lokacin Na’ima ta kalleta, Nuwaira ma ita take kallo tana huci, dan so take Na’ima ta tanka ta mata babban hauka, Na’ima ta juya ta kalli Amira da itama ke tsaye riƙe da hannun saif da ta koma ta kama kafin tace

“Oum Saif, ask ur auntie to stay out of this, tunda ba da ita nake sharing mijin ba” ai ko rufe baki bata yi ba Nuwaira ta kifa mata wani shahararren mari a fuska tana huci kamar kumurciya tace

“Dan durun uwar babanki na miki kama da antynta? Sai dai uwarta ba antynta ba”

Na’ima ta dafe kuncinta shocked, in her life duk zaman da tayi a gidan babanta da daɗi da ba daɗi babu wanda ya taɓa ɗaga hannunsa ya mare ta da wayonta. Kallon Amira tayi tana dafe da kuncinta Amira ta galla mata wani harara tace

“Kallona na uwar me kike yi mayya” ai amira bata kai aya ba taga na’ima ta dage ta ɗaura ma nuwaira mari me shegen zafi a fuska,nuwaira tayi baya ta dafe kuncinta saboda ko kadan batayi tunanin yarinyar nada audacity dinnan ba, Na’ima ta nuna ta da yatsa tana huci tace

“Hands on me again, zan nuna miki ba kowa zaki mara ki tafi a banza ba, you’ll have to explain to the police why you thought beating someone in their own home was acceptable”

kafin nuwaira ta gama farfaɗowa ta ji muryar na’ima da ta juya ta kalli Saif tace

“Go upstairs champ” kamar kuwa jiran tace yake ya zare hannunsa a hannun Amira ya nufi sama da gudu, Amira ta bishi da kallo da maɗaukakin mamaki cause babu gardama babu komai ya wuce saman yaushe har ya san Na’ima ya saba da ita har haka da yake jin maganarta irin haka? Na’ima ta juya ta kalli Nuwaira tana naɗe hannunta a ƙirjinta tace

“kun ma isa a gidana kuzo kuce zaku zageni sannan ku dakeni da wannan filthy hands ɗinnaki as useless as a screen door on a submarine, u bunch of fucking assholes”.

Amira da Nuwaira tsayawa kawai sukayi suna kallon yarinyar because she really took them by surprise sosai sun zaci irin wawuya ce wacce zata na musu kuka,before su gama processing maganar se jinta sukai tana cewa su fitar mata a gida since its not theirs fathers, gidan mijinta ne,Amira kam tsabar shock kasa magana tayi

Na’ima Ta juya ta kalli Nuwaira thats still in shock tace “ke kuma u called me filthy ko? Ni da ke waye filth? Ure throwing hatred towards someone da baki sani ba, someone dat had done nothing bayan keeping a little child safe”

“ke Don uwarki mu kike fadawa magana Don kinga mijina ya aureki yana kwana dake ƙaramar yarinya da ke har kin isa muna faɗa kina fada Don ubanki.” Amira ta katseta cike da bala’i

Wani shegen kallo Na’ima tayi musu, dan bata jin zata barta bata rama ba, a da tana jin nauyin Amira sosai albarkacin Ahmad da saif but not after dis, tayi wani murmushi tana kallon Amira in the eye tace

“badai ubana ba wallahi sannan da kike cewa karamar yarinya naga dai a haka nake jiyar dashi abinda u can never give him every single night, come and see how ur husband behaves when he’s with the ƙaramar yarinya, yake kuma ji in his life he can never do without me”

ta karashe da wani shegen dariyar iskanci wacce ita kanta mamakin kanta takeyi da har take iya sa’insa da wayannan guzumayen matayen har gwara ma Amira, amma Nuwaira shaƙa ɗaya zata mata ta kusa ajalinta, gashi kallon da take mata is like zata ya kashe ta ɗin. Tana gama faɗin haka ta wuce da sauri ta ɗauki wayarta a inda yake zuciyarta na bugawa amma sam fuskarta bai nuna hakan ba ta juya da nufin haurawa sama. Allah Allah take ta haura sama ta shige ɗaki ta rufe ƙofarta ta kira Ahmad

Wani ihu Amira tayi ta finciko rigarta baya kamar taɓaɓɓiya tana mata wasu zunzurutun ashar ta uwa ta uba da ya sa wayar hannunta ya faɗi, Nuwaira ta ƙaraso ta finciki Na’ima daga hannun Amira ta zabga mata wani isashshen mari da hannunta kamar rodi da saida Na’ima ta jita ɗif, kafin ta dawo daga wannan Amira ta sauƙe mata nata suka haɗu suka rufe ta da duka Amira tana kuka da faɗin

“Ƙaryarki ta sha ƙarya, maƙaryaciya ƙaramar makira, shegiya yar iska” ita kam Nuwaira kilar Na’ima kawai take kamar Allah ne ya aiko ta duk da yadda take ƙoƙarin ramawa amma sunfi ƙarfinta tuni wig ɗin kan Nuwaira ya fita sai shegen all back dake kanta da guntun gashinta, Amira na zaune a ruwan cikin Na’ima tana kai mata duka ta ko ina itama Nuwaira haka.

Ɗirkan ta kawai suke kamar sun samu sakwara, zuwa lokacin Numfashin Na’ima ƙoƙarin barin gangar jikinta kawai yake dan ba ƙaramin jimɗa suke mata ba saboda dukkansu sun zuciya da ita ba kaɗan ba, dai dai lokacin yasmeen ta iso gidan da driver dan Ammi forgot ɗaya daga magungunan Na’ima, sai bayan tafiyar Ahmad ta lura tana faɗa kuwa Yasmeen tace ta kawo ta kai saboda sam hankalinta ya ƙi kwanciya da yanayin Ahmad da safen, so take tazo gidan taga ko me yake faruwa, tun kafin ta ƙarasa ƙofar palourn Na’ima take jin ihunta tare da zage zagen su Nuwaira hayaniya dai kaca kaca, ga ƙofar palourn a wangale, zuciyarta ce ta tsinke ta nufi ƙofar da sauri, ta ƙarasa har tana haɗawa da gudu ta shigo palourn, turus ta tsaya kamar gunki tana kallonsu duka kafin ta sake ledar hannunta da jakarta tana faɗin

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” da ƙarfi ganin uban dukan da suka taru suna yi ma Na’ima, ta nufe su da gudu tana faɗin

“Na shiga uku miye haka” amma ina ko ta kanta basu bi na, kukan kura tayi ta riƙo Nuwaira tana ƙoƙarin ɗagata daga kan Na’ima da suka ma jina jina bata numfashi tana kai mata duka, ga ƙasan tiles ɗin male male da jini da ko shakka babu su basu ma lura da shi ba, Nuwaira ta saka duka ƙarfinta da Allah ya bata ta wani irin hankaɗa yasmeen, yasmeen ta yi baya tare da tafiya ta ƙuma kanta da jikin stairs itama take goshinta ya tsage jini ya hau bin fuskarta, for a moment she saw stars ta kurma wani irin ihu da ya dawo da Amira hayyacinta, ta miƙe daga kan Na’ima tana wani irin huci dogon gashinta a zube a jikinta dan tuni mayafinta ya faɗi, Nuwaira ma miƙewa tayi daga jikin Na’imar ta tsuguna ta ɗauki wig ɗinta tana huci da hura hanci, ba tare da sun ko bi ta kan Saif ɗin da suka ce sun zo ɗauka ba ko ita yasmeen ɗin suka nufi ƙofa suka fita a palourn, Yasmeen ta fashe da kuka tana jin raɗaɗin da goshinta ke mata amma wannan tashin hankalin ƙarami ne akan yadda Na’ima ke yashe a wajen ba numfashi, ta tashi da gudu daga kan stairs ɗin ta nufo wajenta ta saka hannu tana jijjigata amma inaa ba numfashi, jinin da ke bin jikinta yana malalewa a ƙasan wajenne ya saka Yasmeen sake ɗaura hannu a kayi ta fasa kuka tana nufar jakarta da ta yasar tare da ledar da Ammi ta aikota ta kawo tana wani kalan kuka kamar zata shiɗe, wayarta ta ciro daga jakar hannunta na shegen mazari ta danna ma Ahmad kira tana wani kuka da sosai, ta koma zauna a ƙasan wajen tana kuka da ƙarfi da kiran sunan yayanta, dai dai lokacin ya ɗaga wayar tare da Sallama muryarsa flat, Yasmeen ta sake fashe masa da kuka wiwi ta ma gagara magana

jin uban kukan da take da baya gane inda ta dosa, ta kuma ƙi natsuwa ta faɗa masa me ke faruwa ya sa ya daka mata tsawa

“Yasmeen!!!!” Ta fashe da sabon kuka tana sheshsheqa kamar zata shiɗe, sassauta muryarsa yayi trying to calm himself yace

“ what happened? Me ya same ki Tell me” kuka kawai take tana janyo ajiyar zuciya cikin kukan tace

“Ka zo gida yaya anty Na’eema ce ..!!” Sai kuma ta sake saka kuka ta jefar da wayar kawai ba tare da ƙarasa ba ta koma kan Na’eema tana taɓa ta tana kuka duk ta gigice, ta ɗaura hannunta a kai tace

“Na shiga uku, wayyo Allah na” tuno wani abu da tayi ya sa ta miƙe da gudu ta nufi ƙofa ta fito tana gunjin kuka fuskarta duk jini ta nufi inda suka yi parking da gudu tana kuka sosai, driver da ya kawo ta dama Ammi ce masa tayi tana bayarwa ya dawo da ita ya sauƙo a motar hankalinsa a matuƙar tashe ganin abinda ke faruwa, sam yasmeen bata san me take ba ta riƙosa tana kuka tace

“Aminu Sun kashe ta ka zo ka taimaka min mu kaita asibiti, innalillahi wa inna ilahi raji’un” jin abinda take cewa yasa ya nufi cikin gidan da Sauri yasmeen bata bi bayansa ba ta ƙarasa gate da gudu tana faɗin su taimake ta a kai Na’ima asibiti, 2 of gate men ɗin ne suka biyota dan taimaka mata suka bar ɗaya a wajen, Yasmeen ta shigo da su har palour tana kuka sosai, Driver Ammi da ya fara ƙarasawa ciki shi ya cicciɓo Na’ima da jikinta ya gama sakewa yayi ƙofa da ita, fuskarta duk ta kumbure dan duka, duk jini ya gama soaking wandonta ya yi male male a tiles ɗin, Sauran suka tsaya suna salati da sallami, Yasmeen ta biyo bayansa da gudu tana kuka.

Fitowarsu compound ɗin yayi dai dai da buɗewa Ahmad gate da akayi bayan wani arnen horn da ya danna, ko parking bai ƙarasa ba ya buɗe motar ya fito leaving the door open, dan the first thing da idanunsa suka kai is Yasmeen dake kuka ga kuma Na’ima da aka ɗauko kamar matatta, ya nufi inda suke da gudu dan he couldnt walk, dakatawa Aminu driver yayi da Na’eema a jikinsa ganin Ahmad, shima yana isowa dab ya ja ya tsaya yana kallon Na’imar then yasmeen, for a moment everything outside his ears went silent, Aminu ya ƙaraso gabansa trying to tell him what happened, hannu kawai yasa ya karɓi Na’ima daga jikinsa hannunsa na rawa dat he couldnt control, yayi wrapping strong arms ɗinsa around her ya fara kiran Sunanta yana tafiya towards motarsa da ita moving faster than he thought is possible, yasmeen da sauran suka bi bayansa, har ya iso motar kiran sunanta kurum yake yakeyi kamar taɓaɓɓe, Aminu ya buɗe masa back seat da Sauri, kwantar da ita yayi a backseat ɗin ya gagara fita a backseat ɗin, ya fara taɓa kumatunta yana faɗin

“Na’ima” amma inaa babu amsa, Aminu da yaga whats happening he’s definitely sure Ahmad bazai iya driving a haka ba, baya ma tunanin driving ɗin ne damuwarsa kawai ta buɗe idanunta da ke a runtse shine damuwarsa, Aminu ya kalli Yasmeen yace

“Shiga muje Yasmeena” ta gyaɗa masa kai har lokacin kuka take ga jiri da take ji itama dan har sannan jini ke bin fuskarta, zagawa Aminu yayi ya shiga mazaunin driver dan a motar Ahmad ya bar key, yasmeen ta buɗe gaba tana ƙoƙarin shiga ta hango Saif daga ta bayan gatemen dake tsaye suna kallonsu a tsaye a gaban ƙofar Na’ima yana kuka, ta kalli Aminu kafin ta sauƙa a motar da gudu ta nufi ƙofar, janyosa tayi ƙafarsa ba ko takalmi ta janyo ƙofar Na’ima ta rufe kafin ta dawo motar tare da Saif ta buɗe gaba ta shiga ta zaunar da shi a ƙafarta har lokacin kuka suke dukansu, shi kam Saif ya gama ruɗewa na abinda ke faruwa, itama duk a ruɗe take, shikam dama Ahmad ba ta su yake ba, dan he can feel yadda duniyarsa gabaɗaya ke pulling away beneath ƙafafunsa, Aminu ya tada motar ya figi motar suka bar gidan a ɗari, Ahmad ya tallafo Na’ima gabaki ɗaya jikinsa hannunsa na rawa yana dudduba jikinta ganin yadda yatsu ke kwance a wuyanta alamun shaqa, ga yatsun Nuwaira goma a both kumatunta, jinin da ke zuba a jikinta zuwa yanzu shi kanshi ya gama ɓata jikinsa da shi, ya ɗago kanta ya ɗaura fuskarsa a kan tata, idanunsa sun kaɗa sunyi mugun jajir zuciyarsa na wani irin abnormal bugawa amma ya gagara sake cewa komai he was numb Har suka iso asibitin.

Aminu na parking yasmeen ta sauƙo da Saif ta nufi cikin asibitin tana kuka da kiran help, Ahmad ya buɗe ƙofar ya sauƙo da Na’ima a rungume a jikinsa da bata motsi ya nufi cikin asibitin shima, tun kafin ya ƙarasa da Na’ima a ƙirjinsa Nurses ɗin da suka taso ɗaya daga cikinsu ta fara shouting stretcher, another one ta ƙaraso tana ƙoƙarin karɓarta a hannunsa, for a moment he didnt want to let go hannunsa shaking suke too badly rigarsa damp da jini, ya sake riƙe ta sosai ba shi da niyyar sake ma nurse ɗin, nurses ɗin da suka iso da stretcher da hanzari suka kalli juna kafin suka kalleshi ɗayar nurse ɗin ta matsa gabansa muryarta softer but firmer tace

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved