⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 53: Chapter 53

A hankali Na’ima ta shiga buɗe idanunta da suka mata Nauyi fiye da misali, ta ɗan lumshesu kafin ta sake buɗewa a hankali tana kallon ɗakin trying to recall inda take, Ammi dake zaune a kujerar kusa da kanta ganin ta motsa a hankali tace

“Na’ima” ta lumshe idanunta ta buɗe tare da kallonta, Ammin ne kuwa ke zaune a kusa da ita, ta fara bin ɗakin da ke cike da kallo, Mami da ta idar da Sallah ta miƙe daga daddumar tana faɗin

“Ta tashi?” Ammi ta gyaɗa mata kai kawai, dan basu ma jima sosai da sauƙa a lagos ba suka taho asibitin ko masauƙi basu ƙarasa ba, Mami ta ƙaraso bakin gadon tana faɗin

“Na’ima” juyawa tayi ta kalli Mami kafin ta motsa bakinta a hankali tace “Na’am”

gabaɗayansu suka saka hamdala cike da farincikin farkowartata, dan tun da aka dawo da ita nan ɗin sai yanzu ta buɗe idanunta, Fadila ta kalli fahad dake zaune a kujera tuntuni Allah kaɗai yasan whats running through his mind, dan shi kaɗai ne yake nan a cikin mazan, Ahmad da Nasir da big Daddy sunje su dawo.
ganin ya miƙe shima zai nufi ƙofa Fadila ta miƙe ta bi bayansa bayan ta miƙawa Yasmeen dake zaune tare da rahama inaya, ta bi bayansa da sauri har waje, suna fitowa waje tace

“Yaya gida zaka?” Ya gyaɗa mata kai kawai yana kallonta yace

“Ke bazaki tafi gidanba?”

“yaya Nasir idan ya dawo zamu wuce”

“Okay” ya faɗa yana shirin juyawa tace

“Zaka dawo nan ɗinne?” Ɗan dakatawa yayi ya kalleta yace

“Wani abinne? Zan dawo mana in maida su Mami da big daddy gida”

“Okay” ta faɗa a hankali ya ɗan tsaya yana kallonta yace

“Akwai wani abinne?” Murmushi ta masa tace

“Dont worry! Bari kawai idan na koma sai driver ya kawo, dama akwai stuffs ɗin da za’a ɗauko a gida, kuma ma da abinci” ɗan harararta yayi dan its clear shi take so yaje ya ɗauko ya ɗanyi ƙwafa yana juya key ɗin motar hannunsa da ya ɗauko daga guest house ɗin big daddy yace

“To ke kina nan ta yaya za’a ɗauko? Ko in maidake ne?” Girgiza masa kai tayi tace

“Ah ah yasmeen ko Rahama sai kuje tare ku ɗauko zan faɗa masu what and what, abinci kuma its ready dama kawowanne kawai” ɗan shiru yayi kafin yace

“Okay su same ni a mota” daga haka yayi gaba abinsa. Fadila ta koma cikin ɗakin tana kallon Yasmeen da rahama, ganin yasmeen na wasa da inaya ita kuma Rahama na waya ƙasa ƙasa sai kawai ta wuce wajen yasmeen ta karɓi inaaya a hannunta tana faɗin

“Zo kiji” biyota tayi suka fito waje, ta fara mata bayanin inda zata aiketa da abinda zata ɗauko, yasmeen ta gyaɗa mata kai tace

“Okay anty fadeela”

“Yauwa ki same sa a waje dan Allah kuyi sauri naji Ammi tace yanzu zaku wuce gida its already 8” Yasmeen tace

“Okay tare da nufar hanyar reception ɗin da wayarta a hannunta dan fita waje ta same Fahad ɗin fadila kuma ta koma cikin ɗakin, ko da ta fito parking space da yake bata san motarsa ba ta tsaya tana kallon space ɗin gashi bata ga ko mai kama da shi ba, har ta juya zata koma ciki ya dallare ta da fitilar mota hakan ya sa ta ɗan kare fuskarta tare da nufo sa ta buɗe gaban motar ta shiga,

tana rufe ƙofar ya ja motar suka bar asibitin without saying a thing.

Tunda aka ɗauko Nuwaira daga gidanta bakinta ya mutu murus, dan bata sake magana a motar ba banda zare idanu kawai da take yi fargaba duk ya gama cika ta ganin suma ba wanda ya sake kulata, sai fai suka yi tafiya mai mugun tsawo for hours kafin su bar main road suka fara shiga outskirt na garin inda babu ma haske sosai gashi lokacin dare ya fara shiga, finally suka iso wani gida mai iron gate a bakin gidan suka yi parking motocinsu guda 2 duk suka sauƙo tare da Nuwaira da yanzu kam wani bala’e’e’en tsoro ne ya shigeta ganin wajen da suka kawo ta baiyi kama da barrack ko station ba kwata kwata kamar irin forgotten warehouse ɗinnan in the middle of nowhere, ta dinga zare idanu babu halin cewa uffan, dragging ɗinta sukayi ciki kamar rago, ta bisu a baya tana hana kanta sakin fitsari dan wajen belong to the nightmares gaskiya, har ciki suka jata suka buɗe wani ɗaki ƙwalli ɗaya da ko window babu a ɗakin suka cilla ta ciki, babu komai a ɗakin sai kujera ƙwalli ɗaya daga ganin ɗakin ka ga ɗakin azaba dan har busashshsen jini itakam ta gani a wasu wajajen a ɗakin.

Ƙarasowa ciki sukayi suna zaunar ta a kujarar suka fara ɗaure mata hannu Nuwaira ta fashe da kuka da kumburarrrn bakinta tana faɗin

“Me na muku? Dan Allah ko mai na muku ku rufa min asiri kuyi hakuri ku ji ƙaina ku yafe min, wallahi bazan sake ba ku min rai dan sonki da Allah da manzonsa” ko kulata basuyi ba, jin bazata yi shiru ba wanda ke ɗaure ƙafafunta ya ɗago tare da wanka mata mari yana faɗin

“Shut up” dan ce musu oga yusuf yayi kar su raga mata at all, so yake gobe idan sunzo shi da Ahmad kar ma su gane kamanninta kafin ma su ɗaura nasu.

Haɗiye kukan Nuwaira tayi tana kallonsa cike da tsoro tace

“Nayi shiru! Nayi shiru”. Yayi wani dariya yana kallon waɗanda ke bakin ƙofar yace

“Za dai kiyi shiru malama, idan mukayi rearranging ɗinki yadda ya kamata” daga haka suka juya suka bar ɗakin. Duk da sun fita amma Nuwaira gagara kuka tayi bata taɓa tsintar kanta a irin wannan tashin hankalin ba, ta ina Sugar zai fara nemaanta? Bayan basu kaita station ko barrack ba? Ta shiga uku ta lalace ita Amira zata ma haka? Ita Nuwaira?

Darennan Nuwaira learnt the meaning of fear, ba su kashe ta ba dan mutuwa ai sauƙi ce amma ta ci ubanta fiye da yadda tayi tunanin zata ciwu, da farko tayi zaton iya ɗaure ta ɗinne da suka yi a ɗakin until da ta ga sun shigo da wasu manyan bulali, ta daku irin dukan da ko sakwara aka ma shi tiɓis zaiyi tsabar laushi, ko da sun gama kilarta sun fita sun barta da ihu da neman agaji basa wuce minti ashirin suke sake dawowa lokacin ta samu ta lallaɓi kanta tayi shiru su sake hawanta da sabon bugu kamar suna filin training, wannan once flawless skin ɗin nata tuni suka faffasa shi, leɓenta ya haye kamar ganda tsabar dukan da ya sha, she’s beating black and blue da in ba farar saninta kayi ba wallahi a kallo ɗaya bazaka ce ita bace, ta tsine ma Amira babu adadi dan bata taɓa zaton Ko me tayi wa Amira zata iya sakawa a mata wannan rashin imanin ba. Haka ta kwana kuka da raɗaɗin jiki da na zuciya tana sake jin tsanar Amira a ranta fiye da wanda ta mata a baya.

Ƙarfe 8:30 na washegarin ranar Yusuf da Ahmad suka iso gidan, sojojin da suke gadin wajen suka shiga sara ma yusuf yayinda yusuf ɗin yayi leading Ahmad har zuwa cikin warehouse ɗin.

Nuwaira na zaune a kujera a ɗaɗɗaure bayan dukan safe da ta gama sha taji an buɗe ƙofar ɗakin, ta ɗaga kumburarrun idanunta ta kalli ƙofa dan a tunaninta ƙari suka dawo su mata amma wa zaga gani Ahmad, kallonsa ta dinga yi ƙuri kamar mayya realization na hitting ɗinta wato shine yasa a ɗauko ta a a mata wannan rashin imanin ba ma Amira ba, ya ƙaraso cikin ɗakin yana bin ɗakin da kallo fuskarsa a ɗaure tamau kamar yadda ta yusuf ke a ɗaure.

Kujeru aka kawo musu, wasu clean kujeru aka ajiye musu a tsakiyar ɗakin, Ahmad ya fara zama shima yusuf ya zauna, kana ganinsu kaga mazaje, Nuwaira tayi wani murmushin takaici tana kallon Ahmad da shima ita yake kallo cause he’s loving what he’s seeing wato yadda suka canza mata fasalin kamanni, ta ɗan girgiza kanta tana kallonsa tace

“Ahma..d” bai amsa ba sai ma leaning da yayi backward a kujerar da yake hands flocked together yana kallonta da expression ɗin da da ace ido na kisa da ya kashe ta da su. Idan ya tuna wai wannan dirty hands ɗinnata ta ɗauka ta ɗaura a jikin Na’ima har ya masa asarar babies ɗinsa ji yake kamar ya ƙarasa ajalinta a wajen but No baya buƙatar hakan at all, ya gyara zamansa yana kallonta idanunsa babu ko single filcker na mercy muryarsa deep and steady yace

“Nuwaira” ɗago idanunta tayi ta kalleshi tana sauƙe ajiyar zuciya,

“I’m giving u a chance to tell me the truth, idan kika kuskura kika min ƙarya, na rantse miki da Allah, i’ll break you until nothing is left, ill make sure kinyi regretting sanin Amira a rayuwarki da yayi leading ɗinki to sanin Ahmad” kallonsa kawai take yi cike da azababben taurin kai, dan ta ma riga ta san tambayar da zai mata, ta san ya riga ya san ta auri Daddy ta san ya san komai, kuma dama yasan alot more than abinda Amira ta sani shiyasa yake rabata da ita tuntuni.

“What did i tell u about my wife the last time? Bance miki ki fita a sabgar matata ba? When i meet u and my father in law a Eko me na ce miki? Let me not see u anywhere near Amira or else ull regret Nuwaira, kin zata wasa nake koh? Kina da audacity ɗin tsallake Amira ki saka these ur filthy hands akan matata, how dare u?”

Kallonsa kawai take yi taƙi tace masa komai. Yusuf ya dafa kafaɗarsa alamun he should calm down, ajiyar zuciya ya sauƙe a hankali yana kallonta cike da tsana ƙarara kafin yace

“Now tell me, Me Amira ta miki? Over shekarun da ta sanki me ta taɓa miki bayan so da kyautatawa? da kike ganin sakamakon da zaki mata shine marrying her Dad? After distroying every peace of her life?”

Har sannnan kallonshi kawai Nuwaira ke yi taƙi tace komai sai ma kauda kanta da tayi, yusuf yayi murmushi ganin taurin kan yarinyar ya wuce inda yake tunani, ya ɗaga murya tare da faɗin

“soldiers” nan take uku suka shigo tare da sara masa, ya haɗe rai yana kallonsu yace

“Prepare her to talk she is not ready” daga haka ya miƙe tsaye ya kalli Ahmad yace

“Muje, bata shirya magana ba idan ta shirya sai mu dawo” Ahmad ya gyaɗa kansa kawai tare da miƙewa dan ji yake kamar ya je da kansa yayi strangling ɗinta har sai ta bar numfashi, Yusuf yayi gaba Ahmad na biye da shi, ganin abinda suke shirin mata Nuwaira ta fara ihu tana faɗin

“Ahmad.. Ahmad na shiga uku dan Allah ka rufa min asiri zan faɗa maka kayi ma Allah ka ce su bari”.

Ko juyowa basu yi ba suka bar building ɗin gabaki ɗayansa, yusuf yace

“Yarinya sai kuma gobe, if u like idan munzo gobe dont talk” shi dai Ahmad bai sake cewa komai ba dan duk abinda yake son sani ya sani game da Nuwaira the only thing da yake son sani shine motive ɗinta daga bakinta, dalilinta na aikata haka, da kuma abinda Amira ta mata da zafi har haka, ita kuma Amira he’ll deal with her so much da bazata sake biye ma ƙawa ba bari ta farfaɗo daga asibitin. Cause tun jiyan ya samu labarin abinda ya sameta a gidan Nuwaira har da sumewan da tayi kwata kwata bata bashi tausayi ba ko ƙanƙani kuwa, ko da aka je picking ɗinta a gidansu bata nan which means she’s still in the hospital.

Daga nan direct Asibiti Ahmad ya wuce dan jiya da ƙyar ya tafi gida daga asibitin, tunda ta farka kowa tana amsa masa sannu da yake mata da murmushi amma shi amsawa kawai tayi taƙi ta kallesa tun jiyan, kwata kwata hankalinsa bai kwanta ba da how she’s behaving, gashi Mami da Ammi na wajen ba damar tambayarta da kyau.

By the time da ya iso asibitin its almost 12 na rana, a hankali yake tafiya towards ɗakinta hannunsa ɗaya a aljihun wandonsa, sai da ya ɗan tsaya kaɗan kafin ya tura ƙofar a hankali.

Da mamaki ya tsaya daga bakin ƙofa yana kallonta ganin ita kaɗai ce a ɗakin, tana zaune a gadon bayanta jingine da pillow, gown ɗin asibiti ne a jikinta pale blue sai hula wanda ya sa she looks harmless and still weak but beautiful, fuskarta looks pale amma calm, hannayenta duka biyu na kan cikinta tana kallon waje ɗaya kamar wacce tayi nisa a tunani.

Tsayawa kawai yayi yana ta kallonta cike da tausayinta, she looks fragile more than ko yaushe, Quietly ya ƙaraso ciki ya rufe ƙofar da doesnt makes sounds ya ƙaraso ciki yana mamakin yadda aka barta ita kaɗai a ɗakin.

Ɗaga idanunta tayi ta kalleshi, ya ɗan mata murmushi kaɗan, ita dai kallonsa kawai take yi idanunta following him as he approach kusa da ita, expression ɗinta guarded babu murmushi babu komai bata ɗaure fuskarta ba kuma bata sake sa ba, babu softness ɗinnan babu komai just silence kawai tana kallonsa.

Ya ja Kujerar gefen gadon ya ya zauna a hankali, muryarsa slow yace

“Babyy” ɗauke idanunta tayi daga kallonsa ta sunkuyar da kanta a hankali tana kallon hannayenta dake kan cikinta, tun jiya da aka ce mata ta rasa babies ɗinta duniyar gabaɗaya take jinsa upside down, ƙaunarsu take ji abinda ko saninsu bata yi ba maybe ma basu gama zama yaʼya ba amma rasasu yayi breaking ɗinta in a way she cant explain, abu bai taɓa mata ciwon wannan ba, not even dukan da suka mata, itakam bazata yafewa Amira da Nuwaira ba.

Jin tayi shiru ya sake ɗan matsowa tare da kiran sunanta “Na’ima” ba tare da ta kalleshi ba tace

“Na’am” kallonta kawai yake ya rasa me zaice mata, in as much as an cutar da ita shima an cutar da shi to ya zasu yi? Allah haka ya rubuta musu, yana shirin fara magana Ammi ta buɗe ƙofar toilet ta fito, ganinshi a zaune daf da gadon ta ɗan harareshi

“Kai kuma sai yanzu?” Ɗan matsar da kujerar yayi baya yace

“ina kwana Ammi” bata kulasa ba ta nufi ƙofa ta fita abinta dan itama ta san they need to talk, sosai Na’ima ke bata tausayi yarinya ƙarama amma tun aure bata huta ba daga wannan sai wanann, bin Ammi yayi da kallo har ta fita kafin ya dawo da idanunsa kanta

“Na’ima..” hawaye kawai taji ya ciko idanunta kiran sunanta da yayi still taƙi ta kalleshi bare tace masa ci kanka, ya tashi daga kujerar ya dawo bakin gadon ya zauna kusa da ita sosai ya kai hannu zai kama hannunta, ƙwace hannunta tayi ta mayar kan cikinta hawaye na gangarowa idanunta, yayi shiru yana kallonta kafin a hankali ya fara magana

“I’m sorry, i dont even know how to start, but i need you to look at me just once kinji” ɗaga idanunta dake cike da hawaye tayi ta kallesa, ya saka idanunsa a cikin nata yana kallon ƙwayar idanunta all he see’s is her pain, rungumota yayi jikinsa a hankali ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana shafa bayanta cike da lallashi he wish he can show shima pain ɗinsa kamar yadda tayi maybe da zai rage masa shima raɗaɗin da yake ji a ransa ya lumshe idanunsa yana jin yadda take kuka a hankali a jikinsa ta riƙe rigarsa,

“I’m sorry, i’m sorry, i’m so, so, sorry baby, ban cika alƙawari na ba, i didnt protect you, i’m sorry”

kukanta kawai take a jikinsa a hankali sai yanzu take jin ɗan dama dama abinda take ji a ranta ta san shima ya damesa as much as ya dame ta tunda ya faɗa mata how much yake son kids but she couldnt help it, more especially idan ta gansa ko she’s alone.

Muryarsa ƙasa ƙasa shima cike da raunin da bata taɓa ji daga muryarsa ba yace

“I dreamt of holding them Na’ima, of being babansu, of seeing u smile da su in ur arms, Amma Allah had another plan, na san laifina ne its my fault kika yi going through all this pain, amma kiyi haƙuri ki yafe min, ki karɓi ƙaddara kinji?”

Girgiza kanta tayi a hankali a jikinsa tana sauƙe ajiyar zuciya, ya ɗago fuskarta daga jikinsa yayi cupping fuskarta yana kallon face ɗinta da lashes ɗinta da suka jiƙe da ruwan hawaye, ya saka hannu ya share mata fuskarta yace

“I’m sorry” gyaɗa masa kai tayi a hankali muryarta a hankali tace “but it hurts” ya ƙarasa share mata idanunta a hankali yana faɗin “Na sani, it hurts me too so much da bazan iya miki bayani ba” ya faɗa yana sake fuskarta a hankali, ta sake shigewa jikinsa ta rungumesa tana sauƙe ajiyar zuciya cause she felt better yanzu and lighter, kuma ta san gaskiya ya faɗa Allah had other plans for them, imanin mutum kuma baya taɓa cika sai ya yarda ta ƙaddararsa mai daɗi ko akasin haka.

Turo ƙofar da akayi ya sa ta tashi daga jikinsa da sauri, yasmeen dake gaba Fahad na biye da ita suka tsaya daga bakin ƙofa, sai kuma fahad ɗin ya juya ya koma waje itama yasmeen ɗin binsa tayi kamar marar gaskiya ta janyo ƙofar ta juya ta kalli Fahad da ke tsaye a bakin ƙofa tana murmushi tace

“Iyye ƙauna” ya harareta yace

“ke kuma gulma” dariya tayi kaɗan tace

“ba wani gulma yanzu da Mami ce ko Ammi fa?” Ya jingina bayansa da bangon wajen yace

“To su ina ruwansu yi zasu yi kamar basu gani ba, ke dai da baki iya gani kiyi shiru bace sai kin tofa” ta tuntsire da dariya tana faɗin

“taɓ, gaskiya ni dai bazan ga abin magana ba kuma ace kar nayi, dama ina ta tunanin Ammi zata ce mun daɗe ashe ma bata ɗakin” shiru kawai yayi yana kallonta dan tun ɗazu Ammi ta aike su sayo fruits wai Na’ima tana so shine sai yanzu, dai dai lokacin Ahmad ya buɗe ƙofar, duk suka juya suna kallonsa komawa yayi cikin ɗakin ba tare da ya ce musu komai ba, Yasmeen ta ɗan kalli Fahad tana gumtse baki, bai kulata ba ya wuce ciki itama tabi bayansa da sauri da ledan fruits ɗin.

Ahmad da Yusuf basu koma wajen Nuwaira a washegarin ba sai the following day, lokacin ba ƙaramin galabaita Nuwaira tayi ba geefen idanunta yai baƙiƙirin, garin duka ma suka ɓalla mata hannu haka suka gyara mata shi a cikin wajen da zunduma ihu har sai da tayi fitsari a jikinta, dan dole suka canza mata kaya dan ma suna sakata sallah in ba haka ba bazasu canza mata kayanba.

Ai tana ganin Ahmad ta fara kuka da faɗin ya ji ƙanta ya fitar da ita wallahi ko Amira yake so taje ta bawa haƙuri zata je ta rantse da Allahnta.

Kujera ya ja ya zauna yana kallonta yace “Kin shirya amsa questions ɗina?” Ta gyaɗa masa kai da sauri

“wallahi zan amsa maka” yusuf yayi wani dariyar mugunta bai ce komai ba, Ahmad na kallonta yace

“I dont need to repeat the questions tunda kin ji su tun jiya” ta share idanunta da hannunta mai lafiya tana sauƙe ajiyar zuciya tace

“Sharrin shaiɗan ne” ya zabga mata wani kallo da yasa ta cigaba da magana

“Am sorry na taso gaskiya da son abun duniya banda godiyan Allah sam..” tayi shiru tana jan hanci kafin ta cigaba “amma kuma its not entirely my fault harda naka, Ahmad tun da muka taso da Amira muke son juna ina sonta tana sona, sai da ka zo ka shiga tsakani na da ita, nasan amira ta rigani saninka amma nina fara furta maka kalmar so,ka wulakantani but me kayi ? U chose Amira instead, duk da ba laifinka bane Uwarta ce ta je har Niger ta biya maqudan kudi aka tirsasa abbu ya saka dole ka yadda ka aure Amira. Sannan dukda blackmail din da Sugar.. sorry Daddynta ya dinga ma Abbu na harkar business dinsu abun beci ba harse da aka hada da kai sunansa gurin boka, dukda haka bance komai ba daga baya da ka aureta na bi ka ka aureni nima amma kaƙi tun lokacin naji bani da buri sai in ƙwace duk wani abu nata da ke sakata farinciki, saboda ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ta sha min gorin ababe dayawa including gidan miji saboda ita ta aure ka ni kuma ina gantali a titi, tunda kai ka gagara auren nawa the next thing da zai girgiza Amira fiye da komai shine auren Daddy, kuma shima daddyn tun tashinmu tare da Amira shine ya fara lalata min rayuwa saboda ya gane ina dason abun duniya ga kwadayi shine ya fara jana har abu ya faru tsakaninmu and it didn’t stop harse da naga na zubar da cikinsa sau 3. Ganin da nayi shi iskanci kawai ya saka a gaba zanyi biyu babu ya saka na qudurci wallahi seya aure ni Don bazeci bulus ba amma sai naga ba aurena yake so yayi ba, shine da na samu cikinsa nayi amfani da shi na sa ya aure ni da taimakon malamai n….”

kallonta kawai Ahmad da yusuf suke cike da disgust shikam yusuf mamaki ne ma ya ishesa, shima Ahmad ɗin kallon da yake mata ne ya sa ta gagara ƙarasawa ta fashe da kuka

“Kuyi haƙuri wallahi duka sharrin shaiɗan ne, ku yafe min wallahi zan bawa Amira haƙuri zata yafe min”

“Ita kuma Na’ima mai ta miki?”

“Babu, wallahi ni babu abinda ta min, kawai itama haushinta da kishinta nakeji sosai..” girgiza kansa kawai Ahmad yayi don magana da Nuwaira ma is a waist of time and energy, she’s far gone, shi kansa yusuf tunanin da yake kenan, Ahmad ya miƙe ya nufi ƙofa, yusuf ya miƙe shima kafin ya kalleta cike da takaici yace

“Ke dai Kinyi asarar rayuwarki, muguwa, azzaluma” yana gama faɗin haka ya nufi ƙofa shima ta fara kiran sunan Ahmad da roƙon yace su barta haka amma ina su kam har sun ƙara gaba.

Dr zarah ta turo ƙofar ɗakin sadiq ta shigo tana riƙe da ƙaramin foodflask, yauma kamar kullum tana sanye da coperate dress da farar doctors coat a sama, agogon hannunta a ɗaure a fari tass ɗin hannunta.

Tana shigowa ta kalli Sadiq dake zaune yana duba book, da mamaki ta tsaya tana kallonsa cause thats actually a very good thing da yake karatu yau sosai taji daɗi tana murmushi ta ƙaraso ciki tare da ajiye flask ɗin a gefe tace

“Good morning bawan Allah” kallonta yayi ya ɗan ajiye book ɗin yana kallonta yace

“Good morning baiwar Allah” tayi murmushi tare da janyo kujera tace

“carry on mana ko ba karatu kake ba?” Ya Girgiza mata kai

“Na gaji” ta ɗanyi murmushi tace

“since ka fara karatu remind me idan na tashi tafiya gobe in kawo maka wani littafi mai daɗin gaske ka karanta” ya sauƙe ƙafafunsa daga gadon yana faɗin

“genre?”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved