Chapter 62: Chapter 62
Suna isa Lagos polo club ɗin Na’ima tayi parking da kyau kafin ta buɗe motar ta sauƙa, shima Ahmad sauƙowa yayi ya buɗe baya yana kallon Saif yace
“Sauƙo” Saif ya sauƙo daga motar ya zaga da gudu ɓangaren Na’ima, Ahmad yayi gaba abinsa ya barsu a baya, har ya ɗanyi nisa yaji basu biyo sa ba, juyawa yayi ya tsaya yana kallonsu, ganin Na’ima ta buɗe backseat ta zaunar da Saif a kujera ta tsuguna tana gyara masa sneakers ɗinsa, ya tsaya shiru yana kallonsu shi bai ma san murmushi yake ba to be honest lips ɗinsa da kansu sukayi curving into the smile, har ta gama ta sauƙo da shi a motar ta rufe ta kama hannunsa suka nufosa, sosai sosai tayi kyau cikin beige high waisted wando da fara tass ɗin shirt button down, glasses ɗinta bata saka a fuskarta ba sai ta saka a saman kanta, she look clean and very very beautiful kamar irin out of magazine ɗinnan, its impossible ka kalleta sau ɗaya ka ɗauke kai. Har suka ƙaraso gabansa kafin ya sauƙe ajiyar zuciya suka nufi cikin wajen tare.
Riders na ta warming up a green field ɗin ko da suka shiga, masu kuɗi da muƙarrabansu duk sune a wajen suna kallo, chatting and sipping chilled drinks. Gurin is screaming kuɗi and lifestyle ɗin masu shi.
Suna zama, Ahmad ya kalleta yace “remember randa nace one day u’ll ride with me?” Ta ɗan kalleshi kafin ta gyaɗa kai, ganin kallon da yake mata ya sa ta yi saurin girgiza masa kai tace
“Nikam na yafe bazan hauba” yayi ƙaramar dariya yace
“Saif ur mimi is a coward she’s afraid of horses” Saif ya juya ya kalleta yace
“Mimi wai? Mimi ko ni fa i dont fear horses ko Papa” ya gyaɗa masa kai tare da miƙewa yana kallonta yace
“Ull ride with me” daga haka ya bar wajen, ta bisa da kallo, kamr ya? ita fa tsoro take ji.
Tana kallonsa aka fito da dawakan, tall, strong horses, da suka sha wanka polished suna ƙyalli, ƙosassu masu shegen kyau, zaɓan ɗaya Ahmad yayi wanda ita kanta Na’ima dake zaune dokin ya burgeta sosai, ta dinga kallonsa har ya hau kan dokin kafin ya juyo ya kalleta ya mata alama da ta zo da hannu, ta maƙale masa kafaɗa tana ɗan dariya dan itakam bata so, sauƙa yayi a dokin ya nufo ta ta miƙe tsaye tana kallonsa har ya ƙaraso yana kallonta ya kama hannunta yana murmushi broadly yace
“Come here, sai fa kin hau” ta miƙawa saif wayarta zuciyarta na pounding ta bi bayansa kamar zata yi kuka. Muryarta ƙasa ƙasa tace
“Ni kam it seems dangerous Allah kuma ana kallonmu fa dan Allah” ya sake riƙe hannunta da kyau yace
“Let them watch”
Sake hannunta yayi bayan sin iso gaban dokin, ya kama dokin ya hau kamar wani prince ko da yake he’s a prince, her prince charming, ta dinga kallonsa miƙa mata hannunsa yayi yana mata murmushi alamun ta basa nata, ta ɗan tsaya tana kallonsa a marairaice ya gyaɗa mata kai a hankali, sai da ta sauƙe ajiyar zuciya kafin ta saka hannunta a cikin nasa a hankali yana kallonta yace
“saka ƙafarki a nan…” ta ɗaura ƙafarta a hankali cike da bin umarninsa, yana murmushi yace
“good! Now hold the saddle” gyada masa kai tayi tare da yin abinda yace, Dokin ya ɗanyi motsi da sauri tace
“ka gani koh” bai san sanda yayi dariya ba yace
“relax mana madam, Numfashi kawai yake” ta gyaɗa masa a tsorace, da just 1 pull yayi lifting ɗinta with ease tare da zaunar da ita a gabansa, scarve ɗinta na swinging a fuskarsa, a ɗosane ta zauna tare ta riƙe reins ɗin tightly, ya lumshe idanunsa a hankali ya buɗe kafin matso da fuskarsa dai dai kunnenta yana zagaye hannunsa a waist ɗinta yace
“Ki sake to yanzu” ta gyaɗa masa kai a hankali, muryarsa a hankali ya sake ce mata
“U trust me dont u” ta gyaɗa masa kai a hankali alamar eh, kafin ta marairaice ta ɗan juya ta kallesa tace
“Idan na faɗi fa”
“Bazaki faɗi ba, i wont let u!” A hankali ya fara tafiya da dokin, yadda dokin ke tafiya da rythm ya sa ta fara ƙoƙarin riƙesa yayi dariya bai ce mata komai ba tana kallon gabanta tace
“Ka sauƙe ni ya isa haka!”
“Kinsan me? Ure too cute when ure scared” runtse idanunta kawai tayi bata sake cewa ba, few seconds later ta ɗan sake jikinta a hankali leaning a jikinsa tana jin ɗan nutsuwa kaɗan kaɗan shi ma yadda jikinsu ke manne da na juna yake saka sa jin wai irin nishaɗi tattare da shi, Ta sauƙe ajiyar zuciya tana jin wani irin nishaɗi itama a zuciyarta muryarta ƙasa ƙasa tace
“This is actually beautiful” ya gyaɗa mata kai yace
“When am with u everything is beautiful” sunyi riding for a while wanda ba ƙaramin zunzurutun kyau sukayi a tare ba kamr ka sace su ka gudu, sai sukayi kamar couples ɗin da aka ciro from wata duniya na daban, Na’ima ta juya ta kalli inda Saif yake ganinsa a tsaye da wayarta yana video yasa tayi dariya tace
“Saif is a gentleman do u know that” yayi dariya shima yana kallon Saif ɗin yace
“Yes he’s”
“Idan Daddy ya dawo gobe, i’ll take him with me muje mu duba jikinsa”
“Allah ya kaimu” ya faɗa yana shafa cikinta da hannunsa dake zagaye a waist ɗinta.
Washegari Monday late Na’ima ta dawo daga school a mugun gajiye, but still wanka kawai tayi ta shiga kitchen ta ɗaura ma daddynta abinci, duk da jirgin 10 na safe ya biyo from russia kuma ba zai iso ba sai kusan 9 na dare amma still zumuɗi yaƙi barinta. Tun jiya bayan sun dawo daga polo suka mayarda Saif gidan Ammi dan kira tayi tayi kan su dawo da shi zai je school gobe, itama Na’ima bata damu sosai ba tunda itama she’ll be in school throughout kuma since daddy sai dare zai iso no need ta tafi da saif zata bari gobe sai su biya su ɗauke shi su je su wuni ma daddy dan gobe bata da intention ɗin shiga school.
Tunda Ahmad ya dawo after isha ya ganta a kitchen ta gama girki tana sakawa cikin flask mai kyau ma daddynta ya koma palour ya zauna bayan ya hau sama ya ɗauko laptop ɗinsa ya ɗaura a ƙafarsa yana aikinsa, already ta riga ta faɗa ma daddy su zasu ɗaukosa she wants to see him first, so ita yake jira ta gama suje ɗauko sa ɗin dan jirginnasu ma ya kusa sauƙa. Ta gama packaging ma daddy abinci a flask ƙarami mai kyau kafin ta saka ma Ahmad nasa ta fito ta ajiye a dining tana kallon yadda duka hankalinsa ke kan aikin da yakeyi, tahowa palourn tayi ta tsaya bayan kujeransa ta zagayo hannunta ta wuyansa tare da ɗan sunkuyowa tace “zaka ci abinci?” Ya sa hannu ɗaya ya riƙe nata dake wuyansa kafin yace
“Kawo min nan” gyaɗa masa kai tayi ta zare hannunta daga jikinsa ta tafi dining ta kwaso abincin ta dawo palour, ta zauna ta tanƙwashe ƙafarta akan carpet tayi serving ɗinsa shi dai yana ta danne dannensa har ta gama kafin ta miƙa masa, ya ajiye laptop ɗin a hannun kujera ya karɓa yana kallonta yace
“Ke fa?”
“Na ƙoshi” ta faɗa tana rufe warmers ɗin, ya kai spoon ɗin abincin bakinsa kafin ya miƙa mata hannu ɗaya, saka nata tayi a nasa tare da miƙewa ya nuna mata kusa da shi, a hankali ta ƙarasa ta zauna, ɗebo abincin yayi ya kai bakinta ta ɗan lanƙwasa kanta a shagwaɓe zata yi magana ya mata alama da she should zip her mouth hakan ya sa ta buɗe bakin ya saka mata, a haka yayi ta cin abincin yana bata tana karɓa har suka cinye, ya sha ruwa ya miƙe ya wuce sama yana faɗa mata ta shirya su je kar su ɓata masa lokaci, ta tattare kayan ta kai kitchen ta ɗauraye wanda suka ɓata kafin ta dawo ta wuce sama da sauri, ɗakinta ta shiga tayi maza ta watsa ruwa ta fito ta shiga shiryawa, tana dab da gamawa ya shigo ɗakin sanye da yadi mai taushi sosai wanda a ido ma kaɗai ka kallesa zaka ga taushinsu dark colour da ya fito da haske da kyaunsa, yana kallonta yace
“baki gama ba?”
“Na kusa” ta faɗa tana ƙoƙarin jan zip ɗin rigarta ya ƙaraso cikin ɗakin yana kallonta ta mirrow har ya ƙaraso dab da ita ya kai hannu ya ja mata zip ɗin yana kallonta yace
“muje?” Ta gyaɗa masa kai da sauri tare da ɗaukar mayafinta da wayarta dake gefen bed bayan ta ɗaura ɗankwalinta very simple da yayi mata kyau sosai.
Suna sauƙowa ta tafi kitchen ta ɗauko abincin ta fito ya miƙa mata hannu ya karɓi basket ɗin da ta sako flask ɗin a ciki yayi gaba ta bishi a baya with just her phone.
Buɗe baya yayi ya ajiye basket ɗin kafin ya zaga ya shiga mazaunin driver dan har ta shiga gaba, ya tada motar suka nufi airport, Na’ima cike da zumuɗin ganin babanta.
Ko da suka ganshi sosai farincikin Na’ima ya ƙaru cause he looks healthier and calmer kamar ba shi ba, ta tafi da gudu ta rungumesa tana masa sannu da zuwa, shafa kanta kawai yayi yana mata murmushi ya kalli Ahmad da ya ƙaraso shima bayan ya gama tsayuwa yana kallonsu ya gaishesa cike da ladabi, ya amsa yana miƙa masa hannu suka gaisa, kafin Ahmad ya karɓi suitcase ɗinsa yana sake masa sannu da zuwa suka nufi motar gabaɗaya. Ahmad ya buɗe masa baya ya shiga tare da ce masa “thank u” murmushi kawai Ahmad yayi bai ce komai ba. Ya zaga ya shiga motar ya tada suka bar Airport ɗin, ita dai Na’ima dama a baya ta zauna kusa da daddynta, banda tambayar jikinsa da all sort of things babu abinda take, shi kanshi daddy he loves new relationship ɗinsa da ita kamar ba ita bace bata taɓa conversing da shi, amma yanzu ba irin tambayar da bata masa ba about his flight, health ɗinsa, ko yaci abinci a jirgi and the rest, fuskarsa ɗauke da murmushi yake amsa mata kafin ya juya ya kalli Ahmad dake driving yace
“Da daddarennan ta sa kun fito ai na so ku bari ku zo gobe kawai da zan kirasu su zo su ɗauke ni ma fa but kuka yi insisting sai kunzo na san ita ta matsa maka koh?” Ya faɗa yana kallon Na’ima da itama shi take kallo ɗauke da murmushi.
“ ba haka bane” Ahmad ya faɗa yana murmushi, Na’ima ta riƙo hannun daddy tace
“I cooked for u, ka gani” ta faɗa tana nuna masa basket mai kyau na kusa da ita ya gyaɗa mata kai a hankali, ta masa murmushi tare da gyaɗa masa kai a hankali itama tace
“U need rest idan kaci abinci ka huta tomorrow zan zo so that in san what the doctors said.” Ya gyaɗa mata kai a hankali yana murmushi yace
“sure” dai dai lokacin Ahmad yayi horn a ƙofar gidan, ya shigar da motar yayi parking da kyau, Buɗe motar daddy yayi ya sauƙo Ahmad ma ya sauƙo ya sauƙe masa suitcase ɗinsa yana kallon Na’ima dake bin compound ɗin da kallo cike da mamaki ganin ba kowa a compound ɗin ta juya ta kalli dad ɗinta ko dai basu san yau dad ɗin zai dawo bane? Gagara haƙuri tayi tace
“Dad su mummy sun san zaka dawo kuwa?” Dad dake magana da Ahmad ya juya ya kalleta kafin ya girgiza mata kai alamar ah ah yace
“Ive been calling she isnt picking her calls tun shekaran jiya” Na’ima ta sauƙe ajiyar zuciya a hankali tace
“Okay” Dad ya juya ya kalli Ahmad yace
“Kar ka damu kuje sai da safe zasu zo su shigar da suitcase ɗin kuje gida dare nayi” Na’ima kallonsa tayi dan so take ta shiga ciki amma yace ah ah suje gida kawai he’ll see them tomorrow. Hakan ya sa ba yadda ta iya haka ta masa sallama bayan ya karɓi basket ɗin hannunta, sai da ya ga fitarsu a gidan kafin ya nufi cikin gidan da flask ɗin ganin Ahmad ya turo masa someone from gate ya shigar masa da suitcase ɗin.
Ya ajiye basket ɗin ɗin da Na’ima ta basa yana ƙare ma palourn dake nan tsit da kallo, har security ɗin ya shigo da akwatin ya ajiye ya fita kafin daddy ya nufi sama. Part ɗinsa ya nufa straight har ya kai hannu zai buɗe ƙofar sai kuma yayi tunanin checking on salma, cause tunda ya tafi bata nemeshi ba shima kuma ko ya kira bata ɗauka.
Ƙofar ɗakinta ya wuce straight yana tafiya a hankali kuma a nutse, a dai dai bakin ƙofar ya dakata dan first sound ɗin zuwa masa yayi faintly, hakan ya sa ya tsaya still a bakin ƙofar, sai a lokacin ya fara ji clearer. Hannu ya kai ya tura ƙofar da ke buɗe slightly, ƙofar ta buɗe without making sound. Sight ɗin da ya gani a gabansa ya sa shi freezing a tsaye da hannunsa still a jikin doorknob ɗin yana kallon salma naked tangled with another man in bed. Kwata kwata ko da wasa basu san da tsayuwarsa a wajen ba har kusan 2 minutes yana kallonsu kafin ya sa hannu ya janyo musu ƙofar tare da jan ƙafafunsa da ke ƙoƙarin kasa ɗaukarsa ya ƙarasa kan kujera ya zauna a palour zuciyarsa na masa wani irin ɗaci.
Rufe ƙofar da yayi ne ya dawo da salma hankalinta ta kalli ƙofa tana ture yazid daga jikinta muryarta a shaqe tace “did u hear that?” dan duk a tunaninta Suhaila ce ta dawo
“what?” Yazid ya ce yana tsareta da idanu. Tashi Salma ta yi tana ƙoƙarin jan guntuwar rigar da ke yashe akan gadon ta ce
“kamar an buɗe ƙofa.”
Da ɗan mamaki yake kallonta sai kuma ya tashi daga kwancen shima. Salma ta ɗauki rigarta ta shige toilet, after some minutes ta fito sanye da rigar bata kalli inda Yazid yake ba ta yi waje ya bita da kallo, Tun da ta hangoshi zaune akan sofa taji zuciyarta ta yi wani irin bugawa da ƙarfin gaske, ta juya da sauri ta kalli ƙofar bedroom ɗinta da addu’ar Allah ya sa kar yazid ya biyota kafin ta ƙarasa shigowa palourn jiki a saluɓe tana kallon Dad dake xaune dafe da kansa a palourn ya yi shiru kamar wanda ya yi nisa cikin tunani, Salma ta ƙarasa gabansa tana kallonsa tana ƙoƙarin ɓoye mamakinta zuciyarta na luguden daka ta ce
“Honey! Yaushe ka dawo? Daman yau zaka dawo?”
Ta jera masa tambayoyin a tare. Ɗago idanunsa ya yi ya kalleta sai kuma kawai ya sake mai da idanun ƙasa ba tare da ya ce komai ba, Salma ta dinga kallon sa ranta cike da tunani da fargabar ko dai ya gan su ne? Ko dai shi ne ya shiga ɗakin.
Tashi tsaye da Daddy ya yi ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, Ya ratsa ta gefenta ya nufi hanyar part ɗinsa without looking at her. Salma ta bi shi da kallo sai kuma ta bi bayansa da sauri zuciyarta na cigaba da lugude, Yana shiga ɗakinsa ya mayar da ƙofar ya rufe sannan ya saka mata key. Salma ta tsaya turus a bakin ƙofar tana sake tabbatar da ya gansu kenan, dakewa tayi ta kai hannu ta fara knocking a hankali tana kiran sunansa cike da rasa madafa da abinyi cause ta san in dai ya gansu to ta ƙare mata innalillahi wa inna ilaihi raji’un, ta ɗauki mintina tsaye a wajen amma sam babu alamar Daddy zai zo ya buɗe, hakan ya sa ta juya ta bar wajen jiki a sanyaye.
A can ɓangaren Daddy duk bugun da take yana jinta ya ƙarasa ya zauna a gefen gado tare da dafe kansa da ke wani irin azababben sara masa, kwanciya ya yi akan gadon jin ya fara jin jiri daga zaune da yake ya lumshe idanunsa yana jin yanda Salma ke cigaba da faman buga masa ƙofa, zuciyarsa na sake hasko masa view ɗin kamar a sannan yake kallonsu.
A stairs yazid yaci karo da suhaila dake shirin haurowa saman dan itama dawowanta kenan, ta dinga kallonsa yadda yake sauƙowa da sauri half shirt buttoned, tsayawa tayi har ya gama sauƙowa kafin tace
“What are u doing upstairs babe” wani kallo ya mata kawai ya nufi ƙofa yana ƙarasa buttoning shirt ɗinsa yace
“What u went out to do without telling me” ta sake baki tana kallonsa har ya shiga ɗakin da yake a gidan ya ɗauko makullin motarsa kafin ya nufi ƙofar fita yana shirin rufo ƙofar ya kalleta yace
“Help me tell ur mum na wuce” daga haka ya fice a palourn, Suhaila ta bi bayansa da sauri compound ɗin da bata gane nufinsa ba. Kafin ya kai wajen motarsa ta cimmasa ta riƙo rigarsa tana juyo da shi tace
“Me ya faru Yazid? Did mummy do anything?”
Harɗe hannayensa ya yi a ƙirji yana kallon ta kamar ba zai magana sai kuma ya ɗan kalli entrance ɗin dan shi damuwarsa yanzu bai wuce ya bar gidan ba dan mummy na fita a ɗakin ya biyota and he understands mijinta ne ya dawo shiyasa yayi saurin komawa cikin ɗakin, suna wucewa part ɗin dad ɗin kuma ya fito ya kama gabansa dan ba haka suka yi da mummy ba bata ce masa mai gidan zai dawo yau ba he dont want trouble, yanzu kuma ga ʼyar ta sake tare shi itama, kuma ba zai iya ignoring ɗinta ba ya wuce ko ba komai tafi uwarta ba da abinda ake so ko ba a gidannan ba zasu cigaba da haɗewa a waje, ya mata murmushi yana kallonta kafin ya ce
“babu komai, kawai zan tafi ne”
Da ɗan mamaki Suhaila ta ce
“tafiya kuma? Akan me toh xaka tafi?”ya matso kusa da ita yana ci gaba da kallon ta ya ce
“Suhaila ina ga mu bari haka. Cause Daddynki ya dawo yanzu, i’ll call u idan na isa gida muyi magana i cant stay when ur dad is here” shiru ta yi tana kallon sa sai kuma ta ce
“My dad is back?” Ya jinjina mata kai yana kallon entrance ɗin gidan kafin yace
“I need to go now.” Gyaɗa masa kai tayi tana kallonsa dan she’s confused ba mummy tace ɗan ƙawarta bane kuma karatu zaiyi a nan to me yasa zai tafi dan Daddy ya zo?” Ta buɗe baki da niyyar masa magana amma taga tuni har ya ƙarasa motarsa ya shiga ya tayar ya nufi gate a ɗari ta bishi da ido har ya fice kafin ta juya ta koma cikin gidan.
****
Daddyn Amira ne kwance gefen gado idanun sa a lumshe hannunsa pressed akan ƙirjinsa, gefen bedside ɗin drugs ne a barbaje sai ledarsu a gefe, hannunsa maƙale da canular wadda aka gama masa ƙarin ruwa. Amira ta buɗe ƙofar a hankali ta shigo tana kallon sa ba tare da ta ƙaraso cikin ɗakin sosai ba, ta tsaya daga bakin ƙofa tayi folding hannunta a ƙirji tana sanye da gown loose one fuskarta babu yabi babu fallasa, dan daddy has been sick for the past 3 days now sai jikin yayi sauƙi sai ya sake rikicewa, tun da ya fara rashin lafiyar sai yau ta shigo dubasa, shima Daddyn buɗe idanunsa yayi yana kallon bakin ƙofar, dan daga mummy har Nuwaira duk wacce ya gani a cikinsu ji yake kamar jininsa na ƙara hawa fiye da hawan da yayi a kwanakinnan, har yanzu ya gagara wrapping kanshi around reality ɗin cewa he has been scammed bare har ya iya musu bayani. Ganin yadda ya zabge a kwana uku sai idanunsa da suka jeme suma looking pale kuma ya ƙi suje asibiti ya sa Amira ta sauƙe ajiyar zuciya a hankali ta ƙaraso cikin ɗakin tana kallonsa amma ta tsaya ɗan nesa kaɗan muryarta a sanyaye tace
“How’s ur body?” Sai da ya kalleta kafin ya gyaɗa mata kai yana cigaba da kallonta ya ce
“Da sauƙi” ta yi shiru tana kallon drugs ɗin da ke gefensa kusan 2 minutes dukansu shiru babu wanda ya sake cewa komai sai kuma ta ɗan kallesa finally tace
“Allah ya ƙara sauƙi” ya gyaɗa mata kai kawai, ta juya zata fita a ɗakin muryarsa low yace
“Amira!” Ta ɗan dakata ta juyo ta kallesa, dai dai lokacin Nuwaira ta buɗe ƙofar ɗakin hannunta ɗauke da cup ɗin shayi da taje ta haɗo masa, Amira na ganinta ta ƙarasa haɗe ranta tare da komawa gefe ta tsaya har Nuwaira ta ƙaraso cikin ɗakin kafin ta nufi ƙofa ta fice a ɗakin, Daddy ya bita da kallo har ta fice kafin ya dawo da kallonsa ga Nuwaira da itama ta haɗe rai tana miƙa masa tea ɗin, miƙewa yayi ya sa hannu ya karɓa zuciyarsa cike da fargaba dan ya tabbata idan Nuwaira ta san abinda ke faruwa ƙila guba kawai zata saka masa a abinci ya ci ya mutu. Ganin sai kallon tea ɗin yake tace
“ka sha mana” ya gyaɗa mata kai tare da cewa “okay” ba tare da ya kai cup ɗin bakinsa ba.
Amira na sauƙowa downstairs, Mummynta da ke zaune tace “kin dubosa?” “Eh” kawai tace ta wuce ɗakinta mummy ta bita da kallo dai dai nan aka danna bell ɗin palour, mummy ta kalli ƙofar kafin ta ɗauke kai tana ƙoƙarin chanza channel aka sake dannawa, miƙewa tayi ta nufi ƙofar ta buɗe tana kallon gateman dake tsaye a wajen, ko kafin tayi tambaya yace
“Ma, madam Amira ake nema wai an kawo mata saƙo” mummy tana harararsa tace
“Inji waye?” Yayi shiru bai ce komai ba, juyawa tayi da niyyar yi ma Amira magana ta ganta tsaye a bakin ƙofar ɗakinta, Amira ta ƙaraso tana kallon mai gafin tace.
“Me?” Ya gyaɗa mata kai cike da girmamawa alamar “eh”
“Ok.” Kawai tace tana jin wani irin sanyi a ranta dan jikinta ya bata Ahmad ne yayo mata saƙo cause in ba shi ba to waye? Mai gadi ya juya ya bar bakin ƙofar ta bi bayansa mummy ta bita da kallo sai kuma tayi ƙwafa ta koma cikin palourn.
Tun kafin ta ƙarasa take hangen manyan mayan motoci a compound ɗin gidan. Mamaki ya sake kama ta dan har ta gane saƙon menene jikinta yayi wani irin sanyi ta ƙaraso tana jan ƙafarta a hankali, ɗaya daga cikin men ɗin dake tsaye wajen ya ƙaraso Ba tare da lura da yanayin da take kallon su ba, cike da girmamawa hannunsa riƙe da clipboard yayi handing mata paper ɗin yana faɗin
“We’re here to deliver your belongings from Mr. Ahmad’s residence. Please sign here.”
Sai a lokacin ta kalle shi, zuciyarta na skipping ta ce
“My belongings?” Ta maimaita muryarta na ɗan shaking, wannan once hope da tayi holding cewa akwai sauran igiya ɗaya tsakaninta da shi ji tayi ya sulale cause him sending everything thats hers from gidansa na nufin ba ya da niyyar sake bata chance ɗin zama a gidansa a matsayin matarsa.
Ta sa hannu ta riƙe clipboard ɗin a hankali muryarta bata fita sosai tace “pls put them inside” suka gyaɗa mata kai kafin suka fara sauƙe kayayyakin suna shigar da su storeroom da ta gwada musu, ta ɗaga idanunta tana kallon sama da ƙoƙarin mayar da hawayen ta kafin ta juya ta wuce cikin gida tana jin wani irin zafi a zuciyarta kuma ta san duk ita ce ta cuci kanta she cant even blame kowa a yanzu, duk wani pride, luxury, boldness, da take da ita na kasancewarta matar Ahmad babu shi yanzu, wani irin raw regret take ji da bata taɓa jin irinsa ba yana sukan ranta ta faɗa gadon ɗakinta tare da cusa kanta a pillow ta fashe da kuka mai cin rai tana faɗin
“Its all over!!”



