⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 7: Chapter 7

“Idan na sake me zakiyi? Ke a tunaninki kin samu handsome and rich guy koh, toh am warning u, Na’ima stay away from him urself or else…”

“Or else what? Sweetheart u wake up with dis energy just to embarass urself, miye ne matsalarki da ni ko sadiq? Mutumin da bai ma sanki ba ure asking me to stay away from him, maybe da shi sadiq ɗin zaki samu kice masa he should stay away from me, tunda am not his level, ure acting like a full time hater on payroll” Na’ima ta faɗa tana miƙewa tsaye

Da bala’e’en mamaki Suhaila take Kallon Na’ima, like a ina ta samo liver?

“Okay.. ni dai na faɗa miki, yafi ƙarfinki, idan har kika ga kin samu someone like sadiq sai dai in bana numfashi ne”

“Toh miss threat, next time kike neman sadiq call 1-800- i dont care, peace, babe”

Daga haka ta wuce kitchen leaving Suhaila shocked cause its been long da ta biye mata, ko da me ta mata kuwa. Miƙewa tayi ta wuce sama fuuu to her Moms Room not minding ko Dad na can since ta san dai zuwa yanzu bai tashi a bacci ba bare fita.

Horn da akayi a gate ya sa mai gadi saurin Ƙarasawa ya buɗe gate ɗin dan tsaf ya gane mai motar, buɗe ƙofar motar tayi bayan tayi parking, ta fito tana zabga ma mai gadin kallon banza ba tare da tace masa komai ba, dogon rigan adire ne purple colour a jikinta, ta sha attach da frontal ɗin ya kwanta ya mata kyau, sai wani siririn ɗan kwali da ta saka a kanta da bai ƙarasa rufe kan nata ba, idanunta sanye da oversized shades da ya kusa cika fuskarta, ta sha kwalliya though not too heavy, tama bakinta kwalliyan nude sai baza ƙamshi take tana taku da heels ɗin da ke ƙafafunta, hannunta riƙe da jakarta ta nufi cikin gidan, Mai gadin ya bita ta da ido, sai kuma yayi ƙwafa ya koma ya zauna bakin gate inda ya tashi

“Aikin kenan, daga oga yayi tafiya wannan basamudiyar matar sai ta ɗebo jiki ta tare, ta ishi mutane da shiga da fita, kai wallahi akwai gyara, inaaa wasu wayewa bata musu rana ba wallahi, wannan gansamemiyar ace wai bata da miji, kuma iyayenta fa ko a jikinsu koh”

Ya faɗa yana danna torch light phone ɗinsa kamar mai magana da wani.

Sau ɗaya ta danna door bell, Mary da ke goge goge a falour ta zo ta buɗe mata, tana ganin itace tayi saurin matsawa daga jikin ƙofan tana gaishe ta cike da ladabi

“Welcome ma, good afternoon Ma”

Ko amsawa bata yi ta nufi sama, zuwa ɗakin Amira, ta tura ƙofar ta shiga, Amira dake kwance saman sofa bacci ya fara ɗaukarta ta buɗe ido jin shigowar Nuwaira sai kuma ta miƙe zaune tana kallon Nuwairan har ta ƙaraso ta ajiye jakarta a gefen bed tana kallon Amiran

“Wai har yanzu kukan kike?”

“Hmm bazaki gane ba Nuwa”

Ƙarasowa Nuwaira tayi ta zauna a gefenta ta dafa ta

“ u dont look good Amira, miye na kuka da sulking bayan tun farko ke kika ja ma kanki Amira, ke kika bashi wannan power ɗin, ba ydda banyi da ke ba akan auren guy ɗinnan amma kika rufe ido kika matsa kika takura kika gama zubar da class ɗinki, har sai da kika saka dad ɗinki a cikin lamarinnan, wanda kinsan ba dan business deal mai ƙarfi dake tsakanin yarwa’s da ku ba a lokacin ba abinda zai sa Babansa ya tirsasa sa ya aureki, tun lokacin nace miki babe mutuminnan bai yi kalar masu mutunci ba bazai bari kiji daɗin rayuwarki ki sakata ki wala ma, amma kika nace, wannan kyau da kuɗi da class da kika maƙalewa kika aure shi taimakon me suka miki yanzu? Ni da bakya jin maganata, nan nace ki shirya in kaiki inda Wlh Ba Ahmad ba ko uban Ahmad ne zai dawo daga lahira dole ya bi Umarninki yayi just as u say, cause u deserve it kinyi ƙarama namiji ya dinga ƙunsa miki baƙin ciki kwata kwata ma shekararki nawa ko 29 ɗin fa baki cika ba amma sam kika ƙi”

Amira ta haɗe rai “Ni nuwaira bana son irin maganar nan, kullum na faɗa miki damuwata sai kin ɗauko maganar nan, u dont need to remind me ai ba mantawa nayi ba nima, kuma Ahmad da kike magana, decision ɗina na aurensa tun ina 24 years is the best decision of my life, hes never Bad, kawai ni na san tsinannun danginsa ne ke son shiga tsakanina da shi, kuma ai yana sona, sosai fa ba kaɗan ba Nuwaira ni na sani, ni da Saif are his everything, kai ba zai ma iya rayuwa babu mu ba.”

Nuwaira na mata wani kallo tace “Haka shi Ahmad ɗin yace miki?”

“Ai ba sai ya faɗa ba, ni na san mijina fiye da kowa, ni tunda nake da shi ma bai taɓa ce min i love you ba, but dat doenst mean baya sona, shi kawai he have a better way of expressing his love ne not all this useless useless talks”

Nuwaira ta galla mata harara “Mayya” dariya suka saka gabaɗayansu

“Yanxu bar musu yaron zaki yi kamar kina tsoronsu?”

“Ke bai fa ce min ya bar yaron a can ba sai da ya tashi tafiya kuma ni wallahi ban lura ba, su sunma isa in bar musu ɗana? Wallahi basu isa ba”

“Ah toh dama ta ina ma zaki fara bari, yanzu yaushe zai dawo?”

“Ni ban san masa ba maybe sai nan da sati biyu, ina ganin call ɗinsa ɗazu naƙi ɗauka to me zaice min?”

“Gwara da baki ɗauka ba gaskiya kamar wata mara class ki ɗauki wayarsa bayan ya gama miki wulakancin da ya ga dama, ni dai bazan daina faɗa miki ba wlh ke kika ƙyale mutuminnan yake abinda ransa ya raya masa, why cant he carry u along a business trips ɗin nasa?, wasu ba haka suke yi da matansu ba? Ko da yake ya san me zaiyi a can ɗin ina zai yarda ya tafi dake ki hana sa sharholiya”

Haɗe rai Amira tayi “ kinga irin maganan da bana so wlh Nuwaira, ƙona min rai yake yi wallahi, wai me zaiyi da wata ne yana da Ni? Ko da kika ga ina saka masa idanu ba wai dan ban yarda da shi bane, kawai dai bana son bada ƙofar da har wani abin zai ɓillo ne”

“Thats cute, but dont let trust turn u into a fool dai, dan Wallahi mazannan na yanzu na madness Dey make dem behave” Nuwaira ta faɗa tana taɓa wayarta

Amira ta koma ta kwanta kan kujera tana kallon Nuwaira dake murmushi tana kallon wayarta

“Nuwaira of Lagos, wanann irin murmushi haka, waya shigo hannu wanann karan? In fara tausayinsa tun yanzu” ta faɗa tana murmushi da kumburarrun idanunta

Nuwaira ta galla mata harara “not ur type of Alhaji, so calm down”

“Ai kam my type of Alhaji wahalan samu ne shi”

“Eh shiyasa kam kullum idonki a kumbure ai tsabar rarity ɗin mijinnaki mtsw”

Amira na dariya tace “oho dai, wallahi Nuwaira, if karma ever catch u….”

“The karma go take me shopping” suka kyalkyale da dariya

“Yanzu ya za’ayi wai batun Saif?”

Nuwaira ta faɗa tana kallon ta

“Ai rakani zakiyi muje in ɗauko abuna tunda cikinsu babu wanda ya tayani naƙuda”

“Now thats my girl, amma ba yau ba ki bari gobe ko jibi sai sun sakankance sun zaci kin bar musu”

“Eh nima ai baxan je yau ba, amma ina dai dai da zamaninsu wallahi, anan zaki kwana ina gobe sai muje”

Nuwaira ta miƙe tana faɗin

“ni dama ai ina nan, ina ga ma har mijinki ya dawo, dan na ce ma Mummy ill be out of town”

Amira ta gyaɗa kai “eh ko ana gobe zai dawo sai ki tafi ba”

Bata kula magabar ba ta nufi ƙofa “ni fa yunwa nake ji ba daga gidan ubana nake ba daman, su waɗannan masu aikin naki dama na kusa korarsu, dan ubansu sai nace su kayo min abinda ya kamata?”

Ta faɗa tana fita a ɗakin, Amira ta koma ta kwanta ta janyo wayar Nuwairah da ta ajiye gefenta………

Kwana uku kenan da Maganar amma haryanzu bata ji yace komai akan abinda suka tata una Wanda hakan ke nufin baya goyon bayan Na’ima ta koma wajen Mamanta a Nigeria, Sosai Mummy ta ji haushin ƙin ɗaukan shawararta da yayi amma sam bata. Nuna ba, ta cigaba da harkokin gabanta, idan Na’ima ta shiga gaishe ta da safe, da murmushi take amsa mata asking of her night, haka idan suna cin abinci ta dinga tambayarta why shes not eating ko da kuwa tana cin abincin, Suhaila ma ta ɗan ja baya da shiga harkar Na’ima da neman ta da bala’i, wanda ita Na’ima bata san dalili ba maybe Mamarta ce ta ce tayi haka bata sani ba, amma for her hakan yafi mata ɗari bisa ɗari.

Yamma ne sosai, street ɗin yayi golden brown saboda rana daya kusa faɗuwa, suna tsaye a drive way ɗin ta jingina da motan sadiq, tana kallonshi da murmushi kwance akan fuskarta thats so obvious

“Wallahi Na’ima” ya faɗa yana dariya “ u know i was just Hanging a saman bishiyarnan, kuma kinsan Umar a lokacin instead of helping me he starting recording me the stupid boy”

Dariya tayi tana kallonsa cike da nishaɗi fararen set na haƙwaranta ƙananu duka a bayyane, sosai ya shagala yana kallonta ya bar dariyar da yake yi yana kallon tata dariyan

“Wai kai ɗin, the same Sadiq bulama da na sani yanzu? Da ke acting so put together and serious ?”

Matsowa yayi kusa da ita, ta haɗiye sauran dariyan tana kallon cikin idanunsa,

“i have layer, sweetheart”

Ta ɗan ja baya kaɗan tare da ƙyafta idanunta

“Sweetheart?”

“Dont mind me” ya faɗa yana ƙare ma fuskarta kallo

Shiru tayi ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers ɗinta, she seem very uncomfortable all of a sudden

“Ni’ima…” ta ɗago kanta ta kalleshi

“Uve been too quite lately, kin tabbata ure okay? Kinsan dai zaki iya faɗa min ko miye ne koh?”

Shiru tayi sai kuma a hankali tace “Everythings not alright sadiq”

“Wannan yarinyar koh?”

“Ba ita kaɗai ba, kowa ma ita da mamanta har da dad”

Kallonta kawai yake yi, ya sake matsowa kusa da ita dis time a little too close, ya sa hannu ya ɗan ja scarve ɗin kanta ya rufe mata gaban gashinta dake waje kafin yayi magana jin ƙarar mota duk suka ɗaga kai suna kallon motar da ya parker just outside her house, ta kalle Sadiq da sauri sai kuma ta mayar ga Dad da ya fito daga motarsa yana ƙare musu kallo, da breifcase ɗinsa a hannunsa, instantly sadiq ya matsa baya da sauri, cike da ladabi yace

“Good evening Sir” dan nan take ya gane shine mahaifinta

Ɗauke kansa Dad yayi, can ƙasa ƙasa yace “Evening” ko Na’imar bai sake kallo ba ya wuce zuwa front door ɗin gidan.

“I should get going” sadiq ya faɗa a hankali yana kallon yadda jikinta duk yayi sanyi da irin amsawar da Dad ɗin ya ma saɗiq

Gyaɗa mishi kai kawai tayi a hankali ta kasa magana

“Ni’eema” ya faɗa yana kallonta

Ta ɗago idanunta ta kalleshi

“Dont panick okay zan kiraki ?”

Sake gyaɗa mishi kai tayi, ya ƙarasa ya shiga motarsa, tana kallonsa har ya bar layin kafin ta nufi entrance ɗin gidannasu.

A tsaye a falour ta tadda Dad, waiting for her, duka hannayensa biyu a goye a bayansa

Tana rufe ƙafar ta ƙaraso falon a hankali jikinta a sanyaye, zata gaishe shi ya rigata

“Waye wannan?”

Da ƙyar ta buɗe baki “Sunansa saɗiq Dad, hes just a friend”

“Ure very stupid, wanann ƙaton ne is just ur friend? How old are u Na’ima?, a boy in my driveway with my daughter kai ba ma a boy ba a Man, a full grown adult, standing close, kinsan how dis looks kuwa Na’ima?”

Shiru tayi ta kasa cewa komai

“Tambayarki nake”

“Dad, hes just a friend trust me, i wasnt doing anything wrong”

“U dont get to decide akan dai dai kike ko ba akan dai dai kike ba a gidana, its me u want to embarass ina?” Ya faɗa yana nuna ta da yatsa

Salma da ta fito daga kitchen jin masifar Dad ta ƙaraso tana faɗin

“What hapoened?” Ta tambaya tana kallob Dad directly, bai amsa ba sai ma cigaba da faɗansa da yayi

“Na baki freedom da yawa ne ma, shiyasa ni zaki nemi tozartawa”

“Daddy…” ta faɗa tana kallonsa Zuwa yanzu hawaye ke sauƙa a idanunta

“Dont Daddy me my friend a wajennan, u think i work all these years for my only daughter to throw herself on boys on the streets”

Suhaila dake zaune a falourn ta wani haɗe rai jin Dad yace his Only daughter

Salma ta matso kusa ta dafa shi

“Pls darling dont shout, ƙaramar yarinya ce, bazata fahimci abinda kake guje mata yanzu ba”

Cire hannunta yayi daga kafaɗansa

“i shouldve listened to u da kika ce in mayar da ita wajen mamanta” sai kuma ya juya ya kalli Na’ima da har lokacin bata bar kuka ba

“Dama ai abinda kike so kenan koh? Tor go and start parking, ure going back to Nigeria, to ur mother”

Daga haka ya wuce sama fuu bayan ya ɗau briefcase ɗinsa.

Yana gama haurawa Mummy ta dubi Naima dake tsaye tana hawaye “sweetheart..” bata jira ta ƙarasa ba itama Na’ima da gudu ta nufi sama, Suhaila tana dariya tace

“U better start parking ur gucci and prada miss new york”

Ko kulata bata yi ba ta shige ɗakinta ta rufe.

_____

Shigowa da hancin motar sukayi cikin gidan bayan security ya buɗe musu gate ganin Hajiya Amira da kanta ke tuƙa baƙar lexus ɗin.

Duk da bata sanar da zuwanta ba amma sanin matsayinta a gidan ya sa shi buɗe mata gate ɗin.

Sai da ta gama parking a ɗaya daga parking spaces dake gidan kafin ta dubi Nuwaira dake kujeran mai zaman banza tana tauna chewing gum, Amira ta buɗe motar ta sauƙo sanye cikin Cream abaya with light embroidery, looking simple but expensive.

Nuwaira ma ta sauƙo fuskarta sanye da glasses suka nufi cikin gidan, door bell suka danna ba’a jima ba aka buɗe musu ƙofar.

Da Mamaki rahama dake falourn ta bisu da kallo, kafin a hankali tace

“Ina wuni? Sannunku da zuwa”

Nuwaira ce kaɗai ta amsa da

“yauwa sannu” kafin ta samu waje kusa da inda Amira ta zauna itama ta zauna tana zare glasses ɗin idanunta, da bin ko’ina da kallo, this is her first time na shigowa gidannan, dan itama Amirar ba wani zuwa take ba.

Miƙewa Rahama tayi ta tattara wayarta da mackbook ɗinta ta nufi sama

“bari in yi ma Ammi magana”

Ba wanda ya amsa mata a cikinsu har ta haura abinta.

Yasmeen ta fito daga kitchen bata ma lura da su ba ta nufi sama, cike da isa Amira tace

“Yasmeen!” Juyowa yasmeen tayi, ta tsaya daga inda take tana kallonsu cike da mamaki

“Ɗauko min Saif ba zama na zo yi ba Sauri nake”

“Bacci yake yi” yasmeen ta faɗa tare da juyawa ta haura sama kayanta.

Nuwaira tayi wata ƙaramar dariya “ eh lallai ai ni baki ce min haka ƙannen Ahmad ɗin suka mugun Raina ki ba, kutt”

Ita dai ƙara ɗaure fuska kawai tayi tana kwatanta abinda zata musu idan tsautsayi ya kawo su gidanta.

Sauƙowar Ammi yasa ta ɗan saki ranta kaɗan har Ammi ta ƙaraso falourn ta zauna tana kallonsu

Gaisheta sukayi a tare, ta amsa a hankali tana tambayar Amira gida.

Jin tayi shiru yasa tace “lafiya dai koh?”

Amira ta gyaɗa kai

“Dama yace min wai Saif na nan shine nace bari in zo ɗauke sa kar ya ishe ku da kuka”

Murmushi Ammi tayi

“ eh kam kin kyauta, amma bacci ma yake yi kar ki damu bai ishe mu ba”

Nuwaira tace “amma hajiya…..”

“And who are u?” Ammi ta tambaya fuskarta babu yabo babu fallasa tana kallon Nuwaira

“Im her friend”

“Then act like one” ta faɗa tana mata murmushi kafin ta mayar da kallonta kan Amira,

“kije zansa su Yasmeen su kawo miki shi har gida” gyaɗa kai Amira tayi duk da ba haka ta so ba.

Ammi ta miƙe “to a gaida gida nagode” daga haka ta wuce sama duk suka bita da kallo kafin Nuwaira ta miƙe fuuuu ta nufi ƙofa itama Amira ta miƙe tabi bayanta da sauri.

Bari nayi Anfani da wannan dama na nuna heartfelt appreciation ɗina to some set of people, the real MVPs ????✨who always drop comments after every chapter, shout out to Rabi’atu Abdul (rii), hafiza saleh bashir (sis), Nanous kitchen, Nanameera matar sadiq, My runaway monita Assalerm, Yasmeen yar makalawanta da girman kujeranki, faɗimatu amaryar Ahmad, Aanaah sister ɗin Amira, Ablaa uwar ɗakin sadiq, Bintu M lawan uwargidan Ahmad,miemer kitchen and more, Alkhairin Allah ya cin muku har inda kuke, tnk u for cheering, commenting, and fueling the journey of N’aima, Sadiq Ahmad and others ????
I see u, i appreciate u, i love you, u guys should take ur flowers ????❤️
#ChapterFam #AuthorLove #TangledHeartsSquad ????????

Chapter 13: one week to everything: dragged by Destiny

Da daddare tana kwance a kan gadonta, tunda ta hauro ɗazu bata sake sauƙa ba, infact makulli ma ta saka ma ɗakinnata, bata san me yake saka ta kuka ba she just cant stop crying, ita kanta ta san abinda take so ne ta samu wato komawa wajen Mami, amma kuma ba ta haka ta so Dad ya amince ba, ta so ya yarda da kansa ba dan wani laifi nata ba, tana kwance lamo a kan gado tunda sukayi waya da Mami wanda Dad already ya sanar mata Next week Na’ima zata dawo wajenta take kwance a wajen, ko Mami sai da ta tambayeta ko lafiya? jin yadda muryarta ta dishe amma tace mata ba komai, kuma da alama Dad bai faɗa mata dalilin da yasa zai maida ita wajennata ba, dan ita kanta mamaki tayi mamaki, buɗe idanunta da suka kumbura tayi ta kalli wayarta da ke ringing a karo na ba adadi, sadiq has been calling tun ɗazu amma ta kasa ɗagawa shi kuma ya ƙi haƙura, janyo wayar tayi bayan ta sa bayan hannu ta share hancinta da yayi ja, ta kai wayar kunnenta tayi Shiru

“Ni’ima” shiru bata amsa ba

“Hey…” ya sake faɗa yana sake rage muryarsa, jin bata amsa ba ya sauƙe ajiyaar zuciya

“Talk to me, say something pls”
kamar jira take ta fashe masa da kuka, da sauri ya tashi zaune daga kwance da yake a kan gadonsa

“Hey , hey , hey , dont do that Ni’imerh, kar kiyi kuka dan Allah, tell me me ya faru?”

Ajiyar zuciya kawai take sauƙewa taƙi tace masa komai

“Kina jina? Ure not alone, babu ruwana da koma miye wani xai ce ko zaiyi, ina tare da ke kinji?”

A hankali ta gyaɗa mishi kai kamar yana gabanta kafin ta buɗe baki a hankali take magana

“Yace zan koma wajen Mamana” ta faɗa tana sauƙe ajiyan zuciyar kuka

Shima ajiyan zuciyan ya sauƙe jin tayi magana

“To bakya son komawa ne? Me yasa kike kuka?”

“Ina so” ta faɗa a hankali

“Okay after that ya miki faɗa ne?”

Ta gyaɗa mishi kai

“eh”

Shiru yayi sai kuma pleadingly yace

“kiyi haƙuri kinji, nine na ja miki, kiyi haƙuri pls”

“Ba kai ka ja min ba, infact am happy zan koma wajen Mami, kawai ba haka na so mu rabu da shi bane, hes Angry”

“He cant stay angry with u for long, ki bari gobe sai ki bashi haƙuri kinji”

Ta gyaɗa masa kai bata ce komai ba

“Yanzu yaushe yace zaki tafi Nigeria ɗin?”

“Next week”

“Okay” kawai ya faɗa yana kallon photo frame ɗinta da ya wanke ya saka a glass ya ajiye a gefen Gadonsa.

Sun ɗan jima suna waya, har sai da tabbatar ta kwantar da hankalinta kafin suka yi sallama.

Ya janyo hoton nata yana kallo sai kuma ya ɗaura a ƙirjinsa ya lumshe idanunsa.

Tashi zaune yayi ya buɗe bedside ya zaro wata waya ya buɗe ta, hotunan Na’ima ne kaca kaca a cikin wayan, ya buɗe messages ya dudduba, whatsapp ya buɗe yaga tana online, Linda ta mata message ita kuma tana typing zata mata reply.

Shiru yayi yana kallon chats ɗin nasu wanda yawanci ma ita kaɗai yake ganin tana magana da ita sai Mamanta da Big Daddy, sai kuma faɗila shima ba sosai ba, ya ɗan haɗe rai kaɗan, ba wani son mu’amalarta da Linda yake ba saboda yaga sun shaƙu sosai, tun ranar da ta bar wayarta a motarsa wanda purposely yaƙi tuna mata cause yana buƙatar wayartata kafin yayi abinda yake son yi wanda bai ɗauke shi lokaci mai tsawo ba before yayi cloning da mirrowing wayar tata, dama yanzu duk wani chats ɗinta, komai tayi typing a wayarta, duk wani scrolling da zata yi a wayarta, and every call ɗinta is mirrowed to wayar dake hannunsa wanda ya saye ta ne dan wannan kaɗai hatta Gps ɗinta.

Fita yayi ya duba last call ɗinta kafin shi yaga Ammi ce ta whatsapp call, gani yayi message ya shiga wayarta from one of her class mate ɗinta na st emerys,

“Na’ima ure ignoring me its not good”

ta buɗe chat ɗin amma bata amsa ba, ya dinga bin chats ɗin yaron ganin kusan kullum sai ya tura mata saƙo na soyayya da ma na gaisuwa, screenshotting yayi ya kashe wayar ya janyo drawer ɗin ya mayar ya jingina da gadon, wayarsa da yake anfani da shi ya janyo yayi dialing number ɗin Mama, tana ɗagawa tun kafin ta fara mita yace

“I’m coming home sati mai zuwa……”

Ajiye key ɗin motar Amira tayi akan console ta zare takalmanta ta ƙarasa ta faɗa kan kujera cike da ɓacin rai, wayarta dake hannunta ta dugurar a kan kujera bayan ta gama karanta saƙonsa

“Mun sauƙa will call when am settled”

Nuwaira da ta ƙaraso itama ta ajiye jakarta fuskarta a mugun haɗe

“Yanzu miye anfanin zuwan da mukayi? Mata ta ce miki wani wai za’a kawo miki shi, ke kuma kin ɗebo jiki mun dawo maimakon ki ce mata ah ah ke ƙafarki ƙafar ɗanki i dont even know why we left without setting that house on fire, wlh kin bani kunya ashe haka kike musu shiyasa suka mugun rainaki”

Amira ta mata wani kallo “dan Allah mu bar maganar nan Nuwa, lallai baki san halin mutanen nan bane, rabu da su ba dai zasu kawo shi ba ai shikenan bar musu ne dai bazan yi ba wallahi”

“Mtswww” Nuwaira ta ja dogon tsaki ta tashi ta wuce sama

Amira ta bita da kallo sai kuma ta miƙe tabi bayanta

Mai aikin da ta balbale da Masifa da safe akan tace sai ta roƙi abinci suke bata ta wuce kitchen da sauri ta shiga haɗa ma Nuwaira Abinci wanda ko Amirar ma ba damuwa tayi da irin wannan ba

Lafiyayyen jollof rice ta zuba mata da kaji ta tsaya bakin steps tana tunanin to sama zata kai mata? Ko jira zata yi ta sauƙo?

Dawowa tayi ta ajiye a falour ta koma kitchen gudun laifi duk da bata san ko hakan da tayi ma laifi bane, sam Basa son su ga Nuwaira a gidan saboda idan bata nan matar gidan ko shiga harkarsu bata yi, iya kaci ta sauƙo taci abinda suka girka ta komawarta sama, ita ba ruwanta ma ko ce musu ga abinda za’a dafa bata yi, kasancewar ƙwararrun masu girki ne.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved