⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 3: CINNAKA ????????????

CINNAKA ???????? (BAI SAN NA GIDA BA SAI YA CIZA)

Story

& Written by

F&F

(Perfect pair ????)

003

Jin shiru bai amsa mata ba yasa ta raba jikinsa da nata tana qare masa kallo yadda yake ta lullumshe idanuwa kamar mai jin barci, a ido ta ga ramarshi mood ɗinshi kamar kullum yadda suka saba ganinsa sumar kansa ta maida baya don ta hanata ganin fuskarsa Masha Allah abin ba’a cewa komai don duk yadda kuke tunanin kyaun gayen nn ya wuce nan duk hasashen mai karatu abinda zan iya cewa shine Kamar shi yayi kansa musamman ƙwayar idonshi wacce ba za’a iya kiranta da baka ba kai tsaye a ynz dae dark ash ce,ta canza bazaka  iya kallon idonshi ba sae kaji wani bugun zuciya ???? musamman ga marasa gsky, ga sajenshi da ke kwance a fuskarsa idan ka ganshi zakayi tunanin ya kai 30years amma he’s not above 26years saboda kamalarshi da kwarjininshi ga small bakinshi reddish fari ne sosai bazamu kirashi da Bature ba,shi ba Balarabe ba ga shi nan dae haka Allah yayi shi abinda zan iya ce maku he’s very handsome irin first class ɗin nan ko halfcast …..

Duk yadda mamanshi ke jero masa tambayoyi ba wacce ya amsa saboda kwata-kwata bashi da yawan magana miskiline sae dae idan shi yaso magana. Kallon A.S.P yayi da maƙiran idanunshi da suka ƙankance a yanzu fuskarsa a matuƙar tsuke take kamar zai yi magana sai kuma ya juya ya kama hanyar fita daga office ɗin babu wanda yayi mamaki saboda sarai sun san waye USMAN (OSEE) mamanshi kaɗae tabi bayansa cikin damuwa….

Dogon numfashi mutumen dake tile saman kujera kamar saƙago tun ɗazu ya ja, ya muskuta tare da soma magana “A.S.P mu ba ƙananan yara bane kuma bugu da ƙari mu musulmai ne waɗanda suka yarda da ƙaddara don ba wannan ne karo na farko da muka fara tsintar kanmu acikin wannan hali ba ka faɗa mana gaskiya shin HAMDA zata dawo garemu ko mu fidda rai kamar yadda ta faru ga ɗan uwanta AJMAL ka faɗa man ina son na san gaskiya saboda bana son na rasata ita kaɗai ta rage man ayanzu amma nace komai ɗacin gaskiya zan ɗauke ta” ayanzu dae bana ce ba baba bani da hurumin baka amsar ‘yarka zata dawo, cigaba da rayuwa ko akasin haka sae yadda Allah ya tsara zai tabbatar amma zamuyi iyakar iyawarmu wajen tabbatar da dawowarta cikin koshin lafiya bi iznilllah, sannan zamu saka matakan tsaro sosai a rugarku domin bada ƙafa gudun ko ta kwana in sha Allah komai zai tafi dai-dai da kyar A.S.P ya kwantar masu da hankali har suka hakura da kanshi ya haɗasu da jami’an shi suka yi masu rakiya har gida duk da OSEE yaso basu matsala amma ba wanda ya damu da hakan saboda kamar yadda nace wnn ba sabon abu bane a wurin su in mutanenshi na kusa yana yin fiye da haka musamman idan ransa ya ɓaci har bakin ƙaramin gida da suke rayuwa a cikinsa abokan rakiyar suka kawosu

Matane duk sunyi cirko-cirko  kowa na cikin yanayin jimami da tausayin kansu amma suna ganin wanda suka sauka daga motar yasa kowa darewa su ka nufi fadar mai gari ana ta ‘yan ƙananan maganganu. Da taimakon mamnshi OSEE ya fito daga motar yana dafe da damtsen hannunshi na dama da ɗayan hannun yayin da  ADDA ( dayar matar) da ARDO (mutumen) ke take masu baya, tun farkon shigowar su ya ƙwala kiran HAMDA!HAMDA! HAMDA!! amma shiru yana kiran sunan yana lalleka ɗakunan kamar zai yi kuka jin taƙi amsashi kai da gani kasan akwae shakuwa a tsakanin su mai girman gaske ” haba HAMDA fushin ne har yanzu baki huce ba ae ya kamata ace ki zubar da makaman ki tarbe ni, ji fa waɗancan wawayen masu kama da inuwar sheɗanu suka kamani ko kin daina so na ne”

Cikin damuwa mamanshi ta share hawayenta cikin son kwantar masa da hankali tace ” APIP (sunan da take kiransa dashi knn) an aike ta ne kai ma kasan ba yadda za’a yi HAMDA ta share ka.kafin APIP da ke murmushi kamar gonar auduga ya samu damar magana ARDO dake tsaye yana kai da kawowa tamkar dogari yace ” kar ma ki fara maimakon ki faɗa masa gsky kin san abunda ya faru a shekarun baya akan AJMAL ko kin…….” Zaburar da APIP yayi ya katse ARDO kamar zai kifa ƙasa dandanan halittar shi ta canza alamun ran ‘yan maza ya ɓaci cikin ficewar hayyaci yace ” kar kuce man ita ma azzaluman can sun kamata ta shiga hannunsu” bai basu damar magana ba don ya riga da yasamu amsarshi akan fuskokinsu bakin shi na rawa ya cigaba da cewa “wai mi yasa mutanen nan suka ta’azzara ma rayuwar mu suka hanamu rawar gaban hantsi wa muka kashe musu, wllhy! wllhy! wllhy!!” jikinshi ya fara wata jijjiga yayinda tari ya hana sauran maganar fitowa ya dafe kirjinshi dake masa bala’in ciwo ga jini na fitowa ta hanci,ta baki ta kunnenshi wnn alama ce ta ranshi yayi kololuwar ɓaci take ya yanke jiki ya faɗi……..

Cikinsu ba wanda bai tsorata ba har da ADDA da tafi su ƙarfin hali sau da yawa APIP na shiga a wnn yanayin har ma fiye da haka lokaci guda kana iya ganinsa daidai, lokaci guda ya canza maka kamar hawainiya (sai a sannu a hankali zamu fahimci waye APIP) amma na yau ya fi basu tsoro kowa yasan irin soyayyar da yake ma HAMDA abin har tsoro yake Bama iyayensu…..

Baya-baya budurwar dake laɓe bayan kofa taja ta kwana da gudu tana hawaye gudu tayi sosai Allah ya kawo ta matsakaicin gidansu zaman mutum ɗaya a haukace ta shiga ta faɗa jikin wata tsigaggiyar mata dake shanya kayanta saman igiya tana kuka yarinya ce da baza ta gaza shekaru 12-15 ba Allah ya zuba mata wani kalar sihirtattan kyau da a kallo ɗaya bazaka iya tantance shi ba sai kana zaune da ita yau da gobe,itama matar ba zamu ce ga ainahinta ba saboda wahalar rayuwa duk ta dafar da ita ta fita hayyacinta murmushi tayi dake fitar da kamalar ta tana shafa bayan ‘yar tata ɗaya tilo da Allah ya bata a duniya tace ” JUHUD Miya faru waya taɓo man ke,kuma ba na hanaki gudu ba??” Mammah kiyi haƙuri yaya bashi da lpy ” kallonta mammah tayi tana tsuke baki mutum ɗaya tasan tana kira da sunan nan  murmushin nasu na manya tayi mai wuyar fassarawa cikin damuwa tace “JUHUD ki kwantar min da hankalinki kinsan ba yau bane yayanki ya fara irin wnn ciwon ba in Sha Allah zai samu sauki yana cikin damuwa kina ganin abinda ke faruwa dasu ga ɓatan ƙanwarshi dole abun ya mashi yawa ki cigaba da taya shi da addu’a zai samu sauki in sha Allah” jinjina kai JUHUD tayi duk da yarinya ce karama tana da tunani irin na manya tana da matuƙar hikima da basira abun har tsoro yake Bama mammah…..

A haukace inna ta kwasa zata fita kiran malaminsu dake kula dashi duk sanda ya shiga yanayin, ARDO ya rike ta shima cikin tashin hankali yace ” baki da hankali a haka zaki fita Bari naje da kaina ku kula dashi kafin na dawo” bai tsaya jin ta bakinsu ba ya fice inna ta koma gurin APIP ke shanye ADDA ta fara bashi taimakon gaggawa matar akwai riko da addini shi yasa take da tsarkakakkiyyar zuciya but surely itama tana cikin damuwa….

Ikon Allah kaɗai yakai ARDO gidan ARZO ( mai maganin su) tsabagen sauri kamar zai kifa ƙasa sai dai samun gidan da yayi  kulle yasa zuciyar sa tsallakewa jikinshi yayi wani kalar sanyi jin kafafunshi basu ɗaukar shi yasa ya nemi dutsen dake kafe kofar gidan ARZO ya zauna yana tunanin rayuwa yana muguwar nadama da tunanin rayuwar shi ta baya ina ma ace lokaci zai dawo baya da ya sauya abubuwa da dama da ayanzu suka zamar mashi matsala da baiyi alaka da wasu mutanen ba ciki harda abokinshi daya ke alakanta halin da yake ciki da shine SILA…..

Called 08167282781

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *