⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 8: Chapter 8

Nuwaira da tayi wanka ta canza zuwa wata free gown ta sauƙo tana kallon plate ɗin da ke rufe, sai kuma ta ƙarasa ta buɗe, wani kallon ahincin tayi kafin ta ƙwallo ma mai aikin kira

“Abincin waye wanann?”

“Na ki ne hajiya, bansan ko sama za’a kai miki ba shiyasa na ajiye miki anan”

Wani irin kallo take mata

“ke mahaukaciyar ina ce zaki ajiye min abinci haka?”

“Kiyi hakuri hajiya baza’a kuma ba”

“Ɓace min da gani, gayyar tsiya, mara hankali kawai”

Da sauri matar ta wuce kitchen ita kuma Nuwaira ta zauna ta janyo abincin tana ci tana danna wayarta har ta cinye tass ta cinye naman ta shanye drinks ɗin da ta haɗo da shi tayi gyatsa ta koma saman kujera leaving the plate a wajen tana danna wayarta.

Amira ce ta sauƙo still in the clothes da suka fita da shi ta zauna

“Wai har kin ci abinci?”

“Eh mana, sai kinga ɗan abincin da suka zuba min a plate kamar na roƙa, mtsw wlh masu aikinki basu da mutunci sam”

“Kiyi hakuri” kawai Amira ta faɗa tana janyo kwalin exotic ta jishi empty ta ajiye bata ce komai ba, kiran da ya shigo wayarta ya sa ta ɗan saci kallon Nuwaira, sai kuma ta miƙe da murmushi akan fuskarta ta ɗaga wayar ta kai kunnenta tana wucewa sama “albii….”

Nuwaira ta bita da harara har ta haura sai kuma tayi ƙwafa

“ba dai ke bakya jin magana ba , munafuka ɗazu ta gama bazata ɗauki wayarsa ba amma saboda ni ta mayar mahaukaciya gashi ya kirata ta ɗauka ba class ba komai mtsw” ta sake jan dogon tsaki…..

Washegari su Yasmeen suka kawo Saif bisa Umarnin Ammi, duk kuma cikinsu babu wanda ya sanar da Ahmad ɗin, basu yi mamakin samun Nuwaira a gidan ba sam, kamar yadda basu samu tarba ba suma basu damu ba, suna ajiye Saif suka juya dan driver na jiransu, Saif ya saka kuka zai bisu, Nuwaira da ke zaune a falon tana kallonsa tace

“kai dan ubanka ka bisu kuje ina? Gidan uwarka zasu koma? Come here my friend”

Kallonta yasmeen ta tsaya yi, rahama ta ja hannunta suka fita a falon, sai da suka shiga mota yasmeen tayi wani ƙwafa

“Ni wlh da bamu dawo da shi ba, ke to shima ba son gidan yake ba”

“Ke dai babu ruwanki, ko kwaɗonsa zasu yi su cinye ba dai mamarsa bace kuma tana kallon ƙawartata?”

Yasmeen ta harareta “Lallai ma, su sun ma isa suyi kwaɗonsa? Ko uwar tasa ce fa? Shima kansa ya san inda ake kula da shi, wallahi da Ammi zata ji shawara ma ta ɗauke shi wallahi”

“To ko zaki faɗa mata ta ɗauko sa ke da kika fi kowa iyawa”

“Kinga irin abinda na tsana kenan wlh shiyasa hira da ke ma is useless”

rahama tayi dariya tana janyo ta “haba twinnie, husainar hassanarta kiyi hakuri toh”

“Bazan yi ba” Yasmeen ta faɗa tana komawa can jikin marfin mota ta kama danna wayarta, itama rahama ɗin wayarta ta ɗauko ta share Yasmeen ɗin”

Shi dai driver Murmushi kawai yake yi.

“Kai yaronnan amma ka iya munafunci, ƙannen uwarka ne su ko na ubanka? Au ashe ƙannen ubanka ne, amma me ka haɗa da su da zaka zauna ka hanani sukuni ka hana uwarka sukuni da kukan banza”

Amira dake kwance tana kallon yadda Nuwaira ta riƙe hannayensa tana masa faɗa ta tashi zaune

“ ki rabu da shi kuka mai dalili yake nema, zonan Saif”

Sake shi Nuwaira tayi ya tafi da gudu wajen Amira ta ɗaga shi ta ɗaura a ƙafarta, ya kwantar da kansa a ƙirjinta yana sauƙe ajiyar zuciyar kuka

“Meyasa baka ji? Zaka je Mary ta maka wanka kayi bacci? Kaga dare yayi”

Maƙe mata kafaɗa yayi

Cike da takaici Nuwaira tana kallonsa tace

“Ni dai wallahi na haihu ɗana ba zai dinga irin wannan iskancin ba haba, kuma wallahi babu shi babu dangin ubansa, yanzu haka ɗan kwana 2 da yayi a gurinsu ne har sun koya masa munafurci banda haka me ya sani da har zai saka mutane a gaba tun da yamma da kukan banza wai granny, ba granny ba granno”

Ita dai Amira bata kulata ba ta miƙe da shi tana kallon hanyar stairs ta ƙwallawa Mary kira, da gudu ta hauro sama ta tsaya a falon saman tana “ yes ma”

“Je ki mishi wanka ya kwanta, ɗazu yaci abincin ne?”

Mary ta gyaɗa kai,

“yes ma, yaci kaɗan”

“Zaka sake cin abinci”

Maƙe kafaɗa yayi, Mary ta saka hannu ta karɓe shi tana jijjigashi suka sauƙa ƙasa….

Satin da ya biyo baya Na’ima ta yi su ne cikin shirye shiryen komawanta wajen Mami Nigeria, duk wani Abu da ta San mai muhimmanci ne ta haɗa abinta, damuwan da ta shiga ma a farko na fushin da Dad yayi sam yanzu babu shi, dan Sadiq sai da yayi duk yadda yayi ta kwantar da hankalinta plus maganar da suka yi da Dad a washegari wanda ya nuna shi baya fushi da ita but it will be of her best ta koma wajen Mami ɗin duk da a baya ma shine ya hana amma a nashi tunanin yanzu Mummy tana da gaskiya kuma itama she wants whats best for Na’iman.

Ranan tafiyarta harda Suhaila a masu rakota Airport, duk da ta san na munafurci ne dan ko rantsuwa tayi bazata yi kaffara ba Mummy ce ta saka ta pretending haka a gaban Dad, tunda tun ranan d abin ya faru babu wanda ya sake shiga harkar juna tsakaninta da ita.

Ɗan rungumeta kaɗan Dad yayi yana shafa kanta “safe flight, make sure kin kira ni in kun sauƙa, greet ur mom and siblings, Allah ya miki albarka” gyaɗa mishi kai kawai take yi wasu hawaye na sake gangarowa tana sharesu

Mummy ma ta zo ta rungumeta “safe flight baby” ita dai gyaɗa musu kai kawai take yi

Sai da Mummy ta ɗan kalli Suhaila ta gefen ido kafin ta ƙaraso tana ƙaƙalo murmushi

“Safe Sis, Allah ya kaiki lfy”

“Thank you” Na’ima ta faɗa tana juyawa zuwa cikin departure terminal ɗin.

Sai da ta yi checking in na suitcases ɗinta a airline counter ɗin, kafin tabi layin security checks and immigration wanda ya ɗan ɗauke su lokaci kafin suyi boarding plane ɗin, with just her carry-on ta ƙarasa kujerarta ta zauna.

Ƙarfin bugun zuciyarta ne ya ƙaru bayan anyi announcing jirginsu zai tashi zuwa Nigeria yanzu, ta mayarda kanta jikin kujera ta jinginar wasu hawaye da bata san na miye ba suka gangaro mata ta lumshe idanunta tana basu daman ci gaba da zuba, ta san zata yi kewar Dad fiye da yadda take tunani duk da differences da suke yawan samu kullum addu’a take masa Allah ya yaye masa wasu abubuwan da yake yi, wasu hawayen suka sake gangarowa daga idanunta dake lumshe, hannu tasa ta share ta buɗe wayarta tama sadiq reply

“zamu tashi”

kafin ta kashe wayar gabaki ɗaya.

The flight was smooth, da yake business class tabi, wanda rabi bacci rabi tunani haka tayi su, her mind was tangled with memories, and her heart heavy.

Ko da suka sauƙa a Doha for layover babu inda taje zama tayi a transit lounge akan kujera kusa da tall windows dake wajen tana riƙe da backpack ɗinta, idanunta da suka ɗan tasa saboda kuka da bacci ta ɗan shafa jin sun mata nauyi, her face looks and feels puffy, ta maida kanta ta jinginar ta lumshe idanunta.

“I’ll be wherever u’re Naima, ko ina rayuwa xata kai ki ull find me close” ɗan murmushi tayi tuno sadiq da kalamansa da tayi. Bata san lokacin da ta ɗauka a wajen tana tunane tunanenta ba, jin annnouncement ta speakers ɗin Airport ɗin yasa ta buɗe idanunta

“Now boarding: Qatar Airways Flight QR1407 to Abuja, Nigeria. Passengers for Gate B22, please proceed immediately.”

Ajiyar zuciya ta sauƙe jin an anbaci jirginta, ta miƙe tsaye da backpack ɗinta ta fara tafiya a hankali towards the gate.

Muryar Pilot ɗin ta cikin intercom shi ya tashe ta a baccin da ya ɗauketa not long ago

“Ladies and gentlemen, we’ve begun our descent into Abuja. Please fasten your seatbelts, return your seatbacks to the upright position, and stow all carry-on items.”

Tashi tayi zaune da kyau tana mutsuka idanunta, ta saka seatbelt ɗinta tare da ɗan runtse idanunta jin uneasyness da discomfort na sauƙan jirgin.

“Ladies and gentlemen, welcome to Abuja. Local time is 5:37AM. The weather is partly cloudy and 25 degrees Celsius…” bata ƙarasa jin me yake cewa ba ta juya ta kalli window ganinsu a ƙasa ta ɗan yi murmushi “Alhamdulillah” ta faɗa a hankali tana zare seatbelt ɗin ta

“Welcome to Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja,” pilot ɗin ya sake faɗa “Local time is 5:43 a.m. We hope you had a pleasant flight.”

A hankali ta miƙe daga kujeranta, ta gyara zaman gyalenta da jakarta a kafaɗarta kafin tabi layin masu sauƙa daga jirgin.

Sai da ta ɗauko suitcases ɗinta a baggage claim kafin ta wuce arrival hall, duk da gajiyar dake tattare da ita, she look effortlessly beautiful without even trying, snickers ɗin ƙafafunta ta sunkuya ta gyara ta miƙe ta sa hannu tana tura cart dake ɗauke da kayanta, tayan cart ɗinne ya ɗan maƙale jikin wani sticker a ƙasan wajen hakan yasa ta ɗan tura da ƙarfi kawai sai yayi jerking gaba, ya jata tayi gaba gabaɗaya pushing mutumin da ke gabanta, hannu biyu tasa ta dafe bayansa wanda shine ya hanata faɗuwa, bayan ta sake cart ɗin, kafin ta miƙe tsaye da Sauri, juyowa yayi tayi saurin yin baya, dogo no sosai yana sanye very clean kaftan, da sunglasses masu duhu a idanunsa, yana riƙe da suit case ɗinsa da hannu ɗaya.

Juyowar da yayi a nutse ya sata sake ruɗewa tana kallonsa ganin yadda yake kallonta cike da annoyance, hannu ya saka ya kaɗe rigarsa

“Im Sorry” ta riga shi magana tana marairace fuska da murmushi akan fuskarta, “didnt meant do bump into you” ta sake faɗa ganin bai amsa ba sai ma kallonta da yake yi duk da bata ganin idanunsa, da ta kasa fassara har yanzu haushinta yake ji? Ko ya haƙura ne?

“Ure in public, try to act like it” ya faɗa tare da juyawa zai bar wajen ta bishi da kallo, what does dat even mean? Haƙuri fa ta bashi Maimakon ya amsa ji abinda kuma yake gaya mata, to hala ita bata san a public ɗin take bane? Me ma tayi toh? No body is above mistakes irin waɗannan, ƙwafa tayi ta bishi da kallo sai kuma ta ja tsaki ta ƙarasa wajen da cart ɗinta yake ta sunkuya ta cire sticker ɗin da ya maƙale, ita sai taga ma kamar ta sanshi a wani wajen but bazata iya tunawa ba his face look somehow familiar.

Driver Mami dake jiranta shi ya kai kayan duka mota, ta buɗe gaba ta shiga tana kunna wayarta, shima driver ɗin ya zagaya ya shiga motar ya tayar suka wuce gida.

Tunda ya fito daga Airport ɗin yake tsaki a ransa, driver ɗinsa dake jiransa ya ƙarasa ya buɗe mai bayan motar ya shiga ya zauna yana ƙoƙarin kunna wayarsa, ɗaga kansa yayi ya kalli window a hankali her face look familiar sure amma baya jin ya taɓa haɗuwa da face irin nata ma, yana kallonta har driver ya saka mata kayanta a mota dai dai lokacin motarsa ta fara tafiya, ya ɗauke kansa daga wajen ya mayar kan wayarsa yana duba available flight da zai bi Gobe zuwa Lagos.

A dai dai gidansa dake Maitama a Abuja driver yayi horn, aka buɗe gate ɗin ya shiga da motar farfajiyar duplex ɗin mai matuƙar kyau, parking yayi a ɗaya daga parking lot 2 dake gidan, ko kafin ya zagayo ya buɗe masa ya buɗe da kansa ya sauƙo yana gyara shade ɗin idanunsa.

He had no idea meyasa yake tunanin that dump girl from the airport, like how on earth zaki ture mutum kuma kina masa murmushi? Ɗan Tsaki ya ja ya wuce sama,

Jallabiya kawai ya zura bayan yayi wanka yayi sallolin dake kansa kafin ya ɗau wayarsa ya kira Amira, har ya katse bata ɗauka ba. Ajiye wayar yayi ya mike ya wuce closet

A shirye tsaff cikin ƙananun kaya, fari ƙal ɗin oxford t-shirt, da beige chinos trousers, ya fito yana zuba ƙamshi, ya ɗauki mukullin motarsa ya fita daga gidan

Sai da yayi magrib da isha kafin ya shigo gidan ya ajiye take away da ya ma kansa a ƙasa ya wuce sama, rigarsa ya zare ya ajiye a kan gado ya wuce toilet, bai jima ba ya fito ruwa na bin body builded jikinsa, da robe a jikinsa, dogon wandon bacci kaɗai ya saka ya feshe jikinsa da turare yana ɗaukar wayarsa da ke ringing ganin Amira ke kiransa whatsapp call.

Bai ɗauka ba ya fito a ɗakin ya wuce downstairs, abincin ya ɗauka ya koma dining lokacin kiran nata har ya yanke, yayi dialing lambarta yana yin bismillah tare da fara cin abincinsa, ringing ɗaya ta ɗauka

“Albi.” Ta faɗa a hankali

Rufe abincin yayi jin kwata kwata ya fice masa a rai ya ɗauki ruwa ta sha ya goge bakinsa ya miƙe tare da ɗaukan abincin da wayarsa ya wuce kitchen dai-dai lokacin da ta sake cewa

“hello..”

“Ina jinki, howre u?”

“Lafiya na ƙalau ina ta kewarka”

Buɗe fridge yayi ya ajiye abincin ya rufe ya ƙarasa ya wanke hannunsa a sinki

“Nace nayi kewarka fa kayi shiru”

“Same here baby girl” murmushi tayi da har yana iya jiyowa

“Yaushe zaka dawo toh?”

“Soon” kawai ya faɗa yana zama a kujeran falon ya ɗau remote yana canza channel

“Allah ya kaimu”

“Amin take care sai na dawo.”

Bai daɗe sosai a falourn ba ya kashe kayan kallon ya wuce sama dan gobe jirgin safe zai bi zuwa Lagos he needs rest.

Ƙarfe 8:40 ya shigo gidansa na Lagos daga Abuja, bin palorn yayi da kallo kafin ya wuce sama, gidan shiru dama abinda yake expecting kenan tunda lokacin tashin matar gidan bai yi ba, falournsa ya buɗe ya shiga ya rufe ƙofar ya ajiye jakar hannunsa a kan kujera yana fara ɓalle buttons ɗin shirt ɗinsa ya nufi bedroom ɗinsa.

Mamaki ne ya kusa kashe shi a tsaye yana bin ɗakin da kallo, wait me yake gani haka is he even dreaming or what?

Nuwaira ce a kwance a kan gadonsa ɗare ɗare tana barci, da wani yan iskan kayan bacci pink a jikinta da tsabar bacci duk ƙafafunta a buɗe, ga plate a bedside drawer na small chops da bata ƙarasa cinyewa ba, da kwalin lemo, wig ɗinta a ƙasa gefen gadon, the audacity da yake witnessing yanzu nearly knocked him off

Juyawa yayi ya kalli Amira da ke sallah wanda ya tabbatar na asuba ne a ɗakin itama da zumbulelen hijab, ya kalli agogon hannunsa tara saura.

Amira da taji buɗe ƙofa a tunaninta Saif ne ko Mary dan Allah Allah take ta idar ta koma bacci, dama ita Nuwaira ta tashe ta Sallar ma bata tashi ba kasancewar sai kusan 3 tayi bacci.

Ta sallame sallan ta juyo da niyyar ganin waye ya buɗe ƙofar idan Mary ce ta faɗa mata kar ta bari Saif ya hauro ya dame ta, bata san lokacin da tayi tsalle ta miƙe tsaye daga kan sallayar ba

“Albi?”

Yadda ta faɗa da ƙarfi ya saka Nuwaira buɗe ido, ta gyara kwanciwarta “wannan wani irin…..” bata ƙarasa ba idanunta suka kai bakin ƙofar ganin can Amira ke kallo idanu a waje, da sauri itama ta miƙe zaune ta janyo duvet tana rufe ƙafafunta itama tana zare idanu than tabbass bata mata warning ɗin da ya mata akan zuwa gidansa ba bare kuma yau sun shiga uku akan gadonsa a ɗakinsa ma ya ganta.

Komai bai ce ba ya juya ya bar bakin ƙofar, Amira ta ɗaura hannu aka tana nufar Nuwaira dake kan gado itama ta rasa me zatayi next

“Nuwa na shiga uku me zan ce masa? Ke ki faɗamin me zan ce masa? Sai da nace miki kar mu zo nan ɗakinsa kika ce in ma bazan kwana ba ke anan zaki kwana kinga abin da kika jawo min koh?”

Nuwaira tayi gyaran Murya jin muryarta ta maƙale

“Ke dillah miye kike abu kamar wani laifi kikayi masa? Sai kace ba mijinki ba ji yadda kike wani rawar jiki, to miye a ciki? Dan mun kwanta a ɗakinsa, ɗakinnasa na gwal ne da baza’a kwanta ba?”

“Haka ma zaki ce min? Bayan kema kinsan yadda muka yi last time akan zuwanki gidannan Nuwa? Kinsan in Mummyna taji sai ta kusa yanka mu daga ni har ke”

“Ta yanka ki dai ke kaɗai, ni me nayi?”

“Haka zaki ce min?”

Nuwaira ta kamo hannunta “kinga Amii, kwantar da hankalinki, kema amma me yasa baki ce min yau zai dawo ba?”

“Nima ai bansan yau zai dawo ba fa bai faɗa min ba “

“Toh kinga ni bari in wuce gida kawai, dont worry babu abinda zai iya, fushi zai ɗan yi kaɗan shikenan ya wuce, ki daina nuna kina tsoronsa dan Allah kamar wata wawuya haba sai kace ke ba mace bace mijinki ne fa zai sauƙo ne”

Ta faɗa tana jan zip ɗin skirt ɗin atamparta da ta ajiye a cikin sif ɗin Ahmad ɗin.

Tagumi kawai Amira tayi tana kallonta, dan ta gagara ma tashi tabi bayansa, har Nuwaira ta gama shiryawa ta yafa ɗan mitsililin gyalenta,

“Bari na wuce Amii, call me when ur oga calm down small, haba shima wlh ya cika ɗaukan komai serious”

Daga haka tayi ƙofa da Sauri ta Sauƙa downstairs ganin baya falourn da Sauri ta fice daga gidan da makullin motarta a hannu.

Buɗe ƙofar da aka sake yi ya saka Amira miƙewa tsaye tana kallonsa ta ja da baya da Sauri amma ta gagara magana, kan gadon ya kalla ganin bata nan yayi ƙwafa ya juya zai bar ɗakin

“Albiii” Amira ta faɗa tana kallonsa da ƙyar ta tattaro kalmomin ma ta haɗa ta ambaci sunannasa.

A fusace ya juyo “Dont call me that, Amira Sau nawa nace miki kar na ƙara ganin wanann yarinyar a gidana?”

Shiru tayi ta kasa magana

“ one simple instruction ‘No Nuwaira in this house’ ba haka nace miki ba but No u even bring her to my space“

“Wallahi fa…”

Kallonta kawai yake cike da dissapointment kafin ya juya ya fara tafiya sai kuma ya dawo

“Duk ranann da na ƙara ganin Nuwaira a gidana, then ull no longer be in the house either”

Daga haka ya fice ya barta a tsaye tana binsa da kallo.

Wallahi bani da lafiya, tun jiya but i dont want to disappoint u guys shiyasa na daure nayi typing ɗinnan, idan kun jini gobe jikin da sauƙi, idan baku ji ni ba ku min uzuri.

Bai dawo gidan ba sai Dare, shima kuma da Sabon ɓacin rai ya dawo, ko kula yadda falon ke zuba ƙamshi bai yi ba ya haura sama duk ransa a dagule, a falon sama ya tarda Amira da Saif a kwance suna kallo, ɗage Saif yayi cak daga wajen yaron ya ɗaga kai ganin babansa ne ya mayarda kansa jikinsa, ba tare da ya kula Amira da ke masa Sannu da zuwa ba ya wuce ɗakinsa da yaron, Amira ta bisa da kallo ganin har kaya ya sauya, toilet ya kaisa ya masa brush ya masa wanka sannan ya shirya sa cikin kayan baccinsa da akwai a ɗakinsa. Yana taje masa gashinsa a gaban Madubi Saif ɗin ya dube shi sai kuma ya shafa fuskarsa “Papa why are u not smiling?” Ɗan Murmushi kaɗan yayi “papa is in a bad mood today” gyaɗa kai yaron yayi kamar ya gane me yake nufi, Ahmad ya ɗauko turarensa ya feshe yaron da shi ya ɗaga shi Sama yaron ya saka dariya, dire shi yayi a kan gado yana murmushi ganin yadda Saif ɗin ke dariya kamar ya masa cakulkuli, haka yake da son wasa, ya zauna gefen Gadon yana kallonsa ya shafa kansa

“Mummy ce ta je ta ɗauko ka daga granny’s place?” Girgixa kai Saif yayi yana ƙoƙarin hawa jikinsa ya kwanta “No aunt Maryam and Yasmeen ne suka dawo dani da granny tace su dawo dani” ya faɗa yana taɓa buttons ɗin rigan Ahmad ɗin

“Meyasa tace su dawo da kai?”

“Saif ma bai sani ba” saif ɗin ya faɗa yana ƙoƙarin sauƙa a gadon

“Okay Saif ya kwanta anan yayi bacci tare da papa” ya faɗa yana ɗagosa daga ƙoƙarin sauƙa da yake yi ya ɗaura sa a kan gadon

“Saif zai je wajen Mary” ya faɗa yana ɓata rai, tsayawa yayi yana ɗan kallonsa kafin ya shafa kansa “Okay” da gudu ya sauƙa a gadon ya nufi ƙofa ya bishi da kallo har ya fice kafin ya miƙe yana ƙare ma bedroom ɗin kallo ƙarasawa yayi ya ɗauki wayarsa ya fita a ɗakin, guess room dake Saman ya buɗe ya shiga Amira ta bishi da kallo dama tasan bazai sake kwana a ɗakin ba ta sauƙe ajiyar zuciya. Sai kuma ta miƙe tabi bayansa, a rufe ta samu ƙofar da key tayi knocking kusan sau uku bai buɗe ba, gagara tafiya tayi ta cigaba da knocking, ya buɗe ƙofar yana ɗaure da towel da alama lokacin ya fito daga wanka, ta gefensa ta ƙare ma ɗakin kallo ganin har ya canza bedshit Yayi gyaran Murya yana goge gashinsa da ƙaramin Towel ɗin hannunsa

“How can i help u?” Marairaicewa tayi tana kallonsa ganin yadda ya mata tambayar kamar bai taɓa saninta ba, ganin bazata amsa ba ya sake ƙofar ya koma ciki ba tare da ya kulata ba ta ƙaraso cikin ɗakin a hankali ta tsaya daga bakin ƙofa kawai ta fashe masa da kuka, lumshe idanunsa yayi ya buɗe bai kulata ba ya cigaba da abinda yake yi, ganin tana tsaye tana kuka still ya zauna gefen bed yana kallonta

Ta ƙaraso ta tsugunna a gefen bed ɗin kusa da shi tana kallonsa “Albi dan Allah kayi haƙuri bazan sake ba” kallonta kawai yake yi yadda take shessheqan kuka, duk yadda ya so nuna mata ɓacin ransa kasawa yayi yana kallonta yace “Amira” ta ɗaga idanunta tana kallonsa, hannunsa ya sa ya kama hannunta ya ɗago ta ya dawo da ita kusa da shi ya zaunar da ita “meyasa bakya jin magana?” Shiru tayi bata amsa ba, “Amira na sha gaya miki times without Number stay away from Nuwaira amma bakya ji, ke a rashin hankalinki har zaki bar ƙawarki ta kwanta a ɗakin mijinki a kan gadonsa? And again why did u went ahead ba tare da amincewata ba kika je kika ɗauko Saif daga wajen Ammi?”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved