Chapter 10: Chapter 10
“Na’imaaa”juyawa tayi taga Faɗila ce ta buɗe ƙofar Main palour ɗin gidan tana sanye da flowy abaya da ɗankwalin abayan ɗaure akanta kamar scarve, da gudu ta ƙarasa wajenta suka haɗu midway suka rungume juna, faɗila na ɗan jijjigata tace “welcome to Lagos sweetheart, my baby girl has finally arrived”
Itama dariya kawai take yi, Faɗila ta kama hannunta suka nufi cikin gidan, kana ganinta kasan tana cikin matuƙar farinciki, dan ba kaɗan ba tayi kewar gida da dangi kwata kwata bata ganin kowa sai on video calls, ba yadda bata yi da Yusrah tazo ba amma taƙi zuwa wai school kuma ta tabbata harda yaya Fahad a masu hana Yusrah zuwa, Naseer dake sauƙowa daga matakala yana murmushi yace “sannu da zuwa Na’ima, an gama ja mana rai ɗin an taho?” Na’ima ta ɗan yi ɗariya “ina wuni?” “Lafiya lau ya hanya?” Ya faɗa yana zama akan kujera a palourn “Alhamdulillah” ta faɗa tana riƙe jakar dake kafaɗarta “To sannu da zuwa Na’ima” jan hannunta faɗila tayi “muje kiyi wanka ki zo kici abinci, am so happy wlh” bin bayanta tayi, wani haɗaɗɗen bedroom ta kaita a nan palorn ƙasan mai matuƙar kyau, babu abinda babu a ciki, tana kallonta tace kiyi wanka bari na shirya miki abinci. Fitowa tayi ta barta a ɗakin ta dawo palour, Naseer da ke zaune ya miƙe yana kallonta “Babe bari naje, daga can i’m meeting Ahmad kinsan halinshi mutumin namu” Faɗila na dariya ta ƙaraso kusa da shi tana faɗin “aikam, haka zaku yi ta zuwa kuna gulmarmu dan ni ban yarda da wannan hanging out ɗin naku ba” hannunta ya kama yayi kissing a hankali yana ɗaukan makullin motarsa “kamar kin sani, aure muke shirin ƙarawa” tayi dariya “shi kam ai kasan pastor ne bai isa ya ƙara amarya ba in ba so yake yi Lagos ta gagaremu duka zama ba” dariya yayi yana kallonta “so yau bazaki ce kar na daɗe ba saboda kin samu abokiyar taya hira koh?” Faɗila tayi dariya “kar ka jima to masoyi, ai kaima kasan ba mai cike space ɗinki sai kai kaɗai” ya ɗan harareta “a baki ba, sai na dawo” “a dawo lafiya” ta faɗa tana kallonsa har ya fita ya ja ƙofar kafin ta wuce kitchen dan haɗa ma Na’ima abinci.
Mai aikinta ta sa ta kai ma Na’ima akwatinta da driver ya ajiye a bakin ƙofar palour, har ɗaki Faɗila ta kai mata abinci, ta zaune gefen gado bayan ta ajiye trayn abincin tana kallon Na’ima dake Sallah, tana Sallamewa ta miƙe tare da Zare hijab ɗinta, Faɗila tace “oya come and eat nasan ure hungry” ƙarasowa tayi gefen gadon ta zauna “not very hungry anty faɗila” ta faɗa tana kallon cikin Faɗila da har ya ɗan fito kaɗan. Faɗila tace “to that little hungry ma bana sonshi” murmushi tayi ta janyo abincin ta soma ci, bata wani ci sosai ba ta miƙe da tray ɗin Faɗila dake danna wayarta tace “ki barshi, zankai” “No bari na kai” “okay!” Faɗila ta faɗa tana kwanciya akan gadon, sai da ta kai tray ɗin kitchen suka gaisa da mai aikin faɗila dake mopping a kitchen ɗin kafin ta dawo ɗakin ta zauna akan sofa tana kallon Faɗila sai kuma ta miƙe ta buɗe jakarta ta ciro wayarta Faɗila ta tashi zaune “let me allow u to rest, in anjima sai muyi maganar school gobe ko ni da ke sai mu shiga school ɗin ko kuma babe ya kaiki dan babu abinda zaki jira, hope ure ready for pan-atlantic”
Ɗan murmushi tayi “ i think so, nadai karanta brochure ɗinsu ya kai sau sau biyar, i just hope i can keep up”
“Keep up? Yanmata kar ki saka ma kanki damuwa ull be fyn, Nigerian schools are about hustle and composure, so ull be fyn as long as u dont dull”
Ɗan dariya tayi “ i dont plan to dull at all anty faɗila just nervous”
Gyaɗa kai Faɗila tayi, “to ai yafi, na miki register for medicals tomorrow, zamuyi printing documents ɗinki, Admission letter ɗinki, scratch card ɗinki, birth certificate duk zaki buƙacesu” gyaɗa kai tayi, Faɗila ta miƙe tana nufar ƙofa “Allah dai ya kaimu goben ive got you, tomorrows gonna be a long day for us”
Binta Na’ima tayi da kallo har ta fita ta ja mata ƙofar kafin ta maida hankalinta kan wayarta da take kiran Maminta da shi.
Da dare tare suka ci abinci gabaɗaya a dining, Naseer na tsokanarta da yar makaranta, hope shes ready for tomorrow, sai dai kawai tayi murmushi.
Bata jima sosai ba ta koma ɗakinta dan so take ta kwanta da wuri since abinda zasuyi gobe da yawa.
Washegari ƙarfe tara Na’ima ta gama shiryawa cikin light denim jeans da farin blouse, da pale pink gyale da yayi matching da snickers ɗinta, folder ɗin da ke ɗauke da duk abinda zata buƙata ta saka a cikin tote bag ɗinta ta rataya.
Faɗila ce ta buɗe ƙofar ɗakin ta shigo ɗakin itama a shirye cikin abaya sage green baby bump ɗinta ya ɗan nuna kaɗan ta cikin abayar wanda sai ka lura sosai kake iya gani
“Kin gama shiryawa?” Ta tambaya da murmushi akan fuskarta tana riƙe da key ɗin motarta da bottle water mai sanyi.
Gyaɗa mata kai Na’ima tayi alamar eh, haka ya sa ta juya ta fita Na’iman ta bita a baya.
Cikin SUV ɗin faɗilar suka fita, a hankali faɗila ke driving smoothly through traffic ɗin lekki, Na’ima na zaune gefenta tana ƙara ƙare ma garin kallo daga inda ta tsaya jiya, “kin tabbatar dai kin ɗauko duk abinda aka ce koh?” Gyaɗa ma faɗila kai tayi tana ciro folder ɗin daga jakarta tana sake dubawa, Admission lettter ɗinta, medical clearance ɗinta, passport photos, printout na GCE ɗinta, receipt na kuɗin makaranta duk intact ta mayarda su cikin folder ɗin sannan ta saka a jakarta.
suna isa pan-atlantic aka buɗe musu gate, Faɗila ta shige da motarta bayan sun ɗanyi security check ɗinsu, Na’ima tabi makarantar da kallo bayan Faɗila tayi parking, ta sauƙe ajiyar zuciya, its official now.
Glasses ɗin idanunta Faɗila ta mayar saman kanta itama tana bin makarantar da kallo.
Admin building suka wuce tare, zama Faɗila tayi ganin layin da ke gabansu, ta buɗe goran ruwa tana sha a hankali, while Na’ima ta jona layin students ɗin da suke jiran turn ɗinsu, har aka iso layinta ta ƙarasa ta bada duka documents da aka buƙata aka mata stamping, basu jima ba suka fito, Naima tana kallon faɗila tace “how do people survive dis without help” faɗila na dariya tace “wasu sai sun koma mota suyi kuka ai da gajiya wallahi” daga nan medical screening suka wuce, inda aka ɗauki fitals ɗinta da duk abinda ya kamata akayi signing off akan clearance card ɗinta, sai da ta karɓi clearance slip ɗinta kafin suje ta ɗauki hoton id card ɗinta wanda zasu dawo su karba in 2 hours, faɗila na kallonta tace “muje mu ci abinci i’m starving” ta faɗa tana shafa cikinta Na’ima ta gyaɗa mata kai dan itama yunwan take ji, wurin cin abinci suka je Faɗila tayi ordering iced habiscus, Na’ima kuma chicken mayo croissant da ruwan gora, faɗila ta kalli heals ɗinta tana ɓata rai
“da na sani da flats na sako”
Na’ima tayi dariya tana cin abinci
“shiyasa i carry my snickers ko ina” suka yi dariya tare, sai da suka je accounting office aka duba course forms kafin a lissafo mata courses da zata ɗauka, starting from Monday, aka bata course handbook, tana fitowa Faɗila da ke waya da Nasir ta sauƙe ajiyar zuciya “saura mana abu ɗaya, muje mu karɓi Id card ɗinki, shikenan kuma na gama nawa sai naki” sai da suka fara duba accounting department block kafin su koma karɓan id card ɗin, sai ƙarfe kusan uku da rabi suka karɓi id card ɗin, tsayawa Na’ima tayi kallon id ɗin, kamar ba yau Dad yace bazata zauna a Nigeria ba amma gashi yanzu officially shes a student in a Nigerian University kusa da Maminta wanda a ko da yaushe zata iya zuwa ta ganta, ta sauƙe ajiyar zuciya tana biye da Faɗila a baya har wajen motarsu, faɗila ta shafa cikinta, “amma na jima ban yi irin gajiyar nan ba” ta faɗa tana tada motar “Na’ima ta jingina kanta da kujera “Allah ya baki lada Anty Faɗila” faɗila ta harareta “toh Ameen, keep me proud dai CGPA ɗinki should be high abeg after all this stress” “yes Ma” Naima ta faɗa tana dariya.
Ranar Monday ta fara attending lectures, wanda sosai take enjoying makaranta, duk da Faɗila tace jjc take, ita da Nasir haka suke tsokananta ita dai sai dai tayi dariya, da safe in ta tashi tayi asuba bata komawa bacci zatayi karatun alƙur’ani zuwa gari ya fara haske, daganan sai skin care ɗinta wanda baya wuce cleanser, lip balm, da vanilla body mist da take ma jikinta, zuwa 7 da kaɗan yawanci ta shirya cikin either Abaya ko kuma wide leg jeans da shirts sai gyalenta da signature tote bag ɗinta da take tattara komai nata a ciki kama daga notebooks ɗinta, ipad ɗinta da pen, starnley cup ɗinta, da another water bottle sai ƙaramin pack na snacks, zuwa 7:30 ta bar gida wanda driver ke sauƙeta makaranta kullum, ƙarfe 8 take fara first lecture ɗinta bata taɓa latti ba, sosai Nasir da faɗila ke jin daɗin how serious she’s da abinda ta saka a gabanta wato karatunta, zuwa ƙarfe 3:30 driver ke komawa ya ɗauko ta daga makaranta, sometimes idan bata gaji sosai ba kuma sai ta shiga kitchen tana taya cook ɗin aiki da sake koyan different dishes na Nigeria banda waɗanda ta iya, idan kuma a gajiye ta dawo sai dai kawai ta yi wanka ta ci abinci da sallah tabi lafiyar gado. Ba ƙaramin daɗin zama da ita faɗila take ji ba dan kwata kwata bata da matsala, abinda ke gabanta kawai shi take yi,kuma tana ɗebe mata kewa sosai.
sati biyu da fara school ɗinta Fahad ya zo wanda a ranan ya koma bayan ya ga how smoothly shes blending in, duk da karatun accounting ba sauƙi amma sosai ta mayar da hankalinta gabaki ɗaya kanshi, ta bashi dukkanin attention ɗinta, zuwa yanzu ta rage damuwa da shirun sadiq, duk da takan tuna shi sometimes kuma tana matuƙar son jin ko lafiya yake amma ba yadda zatayi sai kawai ta tattarashi ta ajiye gefe ta maida hankalinta akan karatunta.
Yauma kamar kullum a hankali ta buɗe idanunta bayan alarm ɗinta ya kaɗa, lumshe idanunta tayi ta sake buɗe su kafin ta miƙe zaune a hankali tana mutsuka idanunta, ta sauƙa akan gadon ta wuce toilet, da alwala ta fito ta shinfiɗa darduma ta tada sallar asuba, tana idarwa ta buɗe Qur’ani a wayarta ta karanta just few pages inda ta iya, kafin ta miƙe ta linke sallayar ta ajiye ta wuce bayi tana hamma.
Zuwa 7:17 har ta gama shiryawa cikin abaya mai kyau da tsada da suka siya last week tare da faɗila, ta cire ipad ɗinta daga charge ta saka a jakarta, ta ɗauko hand cream ɗinta ta saka a jakarta da sauran tarkacenta.
A palour ta tarda Faɗila a tsaye a dining tana haɗa ma Nasir breakfast, zata kai masa sama cause zai fita shima very early today,
“Ina kwana Anty Faɗila Maman unborn” ta faɗa tana zama akan kujeran dining ɗin “lafiya lau, yau har kin shirya da wuri haka?” “Eh wlh ive something to do ne kafin na shiga aji yau shiyasa” “eyya” ta faɗa tana ɗaukar tray ɗin abincin da ta haɗa ma Nasir “bari in kaima babe abinci, hes also going out early today” “toh” Naima ta faɗa tana haɗa ma kanta shayi har Faɗila ta haura sama, har ta gama shan shayin bata sauƙo ba ta miƙe ta wuce kitchen, box ɗin snack ɗinta ta saka a jaka tana kallon lunch box ɗin Nasir da faɗila ta haɗa masa tayi murmushi kawai tana fita a kitchen ɗin, a palour ta tadda su Suna riƙe da hannun juna suna magana ƙasa ƙasa, ta tsaya a dining tana kallonsu, Nasir ya dube ta “yau har kin shirya Na’ima” gyaɗa masa kai tayi ta gaishe shi ya amsa mata yana kallon Faɗila yace “sai na dawo?” Ta gyaɗa mishi kai sai kuma tace “Laa na manta da abincinka”ta wuce kitchen da sauri, murmushi kawai yayi dan yasan bai isa yace bazai tafi da shi ba, har ta dawo ta kama hannunsa da saka masa kyakkyawan lunch box ɗin “thank you” ya faɗa a hankali, kafin ya kalli Na’ima “muje toh sai nayi dropping ɗinki tunda hanyar zanbi” “ah ah yaya Nasir ill follow d driver pls dont bother” “kuje ya sauƙe ki mana shima Yusuf driver din sai ya huta in yaso sai yaje ya ɗauko ki”
“Toh” kawai tace ganin har ya nufi ƙofa ya fita tabi bayansa, Faɗila na shafa cikinta tace “sai kun dawo”
A mota Nasir yana ta janta da hira da tambayar yadda karatunta ke tafiya ganin taƙi sakin jikinta har suka kusa isa makarantar, wayarsa dake jone da speaker ɗin motar yayi ƙara ya ɗan saci kallon wayar ganin Ahmad ya sa shi murmushi kaɗan ya ɗaga wayar dai-dai yana shiga gate ɗin makarantarsu “How far?” Ya faɗa yana ɗan dariya kaɗan “kana ina ne?” “Sorry na ɗanyi dropping ƙanwar matata a school ne am on my way yanzu zaka ganni” daga ɗaya bangaren yace “and u think ill wait for u?” Nasir na parking a bakin department ɗinsu yayi dariya “Ka dai yi haƙuri ka jira ni ɗin am on my way Allah” bai amsa ba sai ma kashe wayar da yayi. Naima da har ta sauƙa a motar ta rufo motar ta tsaya dai dai window ɗin “thank you so much yaya Nasir” “welcome, ayi karatu da kyau, sai kin dawo” daga haka ya ja motar yayi gaba ita kuma ta ƙarasa class.
Ƙarfe uku dai dai ta gama lecture ɗinta na rannan a gajiye ta fito tana tafiya a hankali zuwa parking space, turus ta tsaya fuskarta ɗauke da maɗaukakiyar mamaki tana kallonsa kamar a mafarki, ta gagara ƙara ko taku ɗaya, kallonsa kawai take dan ta kasa fahimtar ta yaya? yana tsaye jingine da motarsa hannunsa duka biyu a aljihunsa yana kallonta da murmushi ɗauke a kan fuskarsa. “Sadiq?” Ta faɗa cike da mamakin yaushe ya zo Nigeria sannan ya akayi ya san tana lagos har kuma makarantar da take.
Da ƙyar ta ɗauke kanta daga gare sa ta mayar kan Yusuf da ke parking motarsa inda ya saba parking idan ya zo ɗaukarta, ɗaga ƙafarta tayi a hankali ta ƙanƙame jakarta a kafaɗarta ta cigaba da tafiya not towards Sadiq but Yusuf driver, hakan ya sa murmushin dake ɗauke a fuskarsa ɓacewa ya yi saurin barin jikin motar ya biyo bayanta
“Ni’eema wait pls”
Ƙara sauri tayi taƙi tsayawa yayi saurin shan gabanta
“Ki saurare ni nace, why are u behaving this way?”
Kallonsa kawai takeyi ta kasa magana, sai kuma ta raɓa gefensa zata wuce ya sake tarewa, ita abinda take gani a cikin idanunsa shi ta gagara ganewa, ta sake ƙoƙarin wucewa ya sake shan gabanta, Yusuf da ya lura da abinda ke faruwa ne ya ƙaraso wajen a tunaninsa ko kawai random person ne ya biyo ta yake ƙoƙarin mata magana “Malam lafiya? Ya zaka tare mata hanya kuma tana ƙoƙarin wucewa kana sake tarewa?” ko kallonsa bai yi ba sai ma kallon Na’ima da yake yi cike da mamaki ganin taƙi magana sam wanda shi ya rasa dalili, yusuf ya ƙarasa ya buɗe bayan motar ya dawo yana kallonsa yace “to bata wuri ta wuce dan Allah” still Sadiq ko kallonsa bai yi ba” cike da mamaki yusuf yake kallonsu ganin itama akwai space a gefe da zata iya bi ta wuce amma ta tsaya a wajen ta sunkuyar da kanta sai kawai ya koma gefe ya tsaya yana kallon ikon Allah
“Ni’eema” kamar dama jira take yayi maganar ta raɓa ta gefensa ta wuce ta shige motar da Yusuf ya buɗe mata, da sauri sadiq ya taho da niyyar sake mata magana yusuf ya rufe ƙofar “Sai kuma kayi haƙuri haka malam” ya faɗa yana wucesa ya zaga driver sit ya shiga ya tada motar ya bar harabar wajen, bin motar da kallo sadiq yayi shocked, he was frozen for some seconds cause ba abinda yayi expecting kenan ba he was expecting something else, sai kuma ya cije lips ɗinsa ya shafa lallausan gashin kansa ya dunƙule hannunsa ya naushi iska, kafin ya juya ya nufi motarsa ya shiga ya tada ya bar makarantar a guje.
Har suka isa gida kanta na kife akan ƙafafunta, ita kanta bata san dalilin ƙin kula sadiq da tayi ba, a yadda tayi kewarsa tayi zaton idan ta gansa farinciki xata yi sosai sai kuma ta samu kanta da akasin haka, tunani kala kala ne a zuciyarta na farko ghosting ɗinta da yayi for weeks bayan lafiyarsa ƙalau, na biyu kuma yadda ya san inda take, ya san tana lagos da makarantarta har ma da department ɗin da take, bayan tun barinta Newyork sau biyu suka yi magana da shi kuma lokacin tana Abuja bata fara ma maganar zuwa lagos ba, sannan hes not in contact da kowa nata bare tace su suka faɗa masa. Haka kawai taji zuciyarta na bugawa ba ƙaƙƙautawa.
Ta lumshe idanunta a hankali tana jinginar da kanta da seat ɗin motar, shi dai yusuf yana kallonta ta mirrow “sai hakuri hajiya” abinda yake ta nanatawa kenan ganin kamar duk mood ɗinta ya canza ba haka ya saba ganinta ba.
Yana parking ta buɗe motar ta sauƙa ta wuce cikin gida, shima ya rufe motar ya wuce wajen jamilu mai gadi dan faɗa masa abinda ya faru yau a makarantarsu hajiya.
Wajen ƙarfe shida da rabi tana zaune akan kujeran gaban madubi lost a cikin duniyarta wayarta yayi ƙara ta ɗan kalli wayar ta kauda kanta, zuwa yanzu ya kirata ya kai sau biyar, ya mata messages on whatsapp wanda ko buɗewa bata yi ba, har kiran ya katse tana zaune tana kallon sunansa da ke yawo a screen ɗin da hoton da ta saka a caller id ɗin wanda sukayi tare cikin jackets dukansu a newyork shine ma ya musu selfie dukansu da murmushi a fuskokinsu, message ɗinsa ne ya shigo wanda tana iya karanta shi akan fuskar wayarta
“Pls, talk to me” sai kuma wani ya sake shigowa
“U look beautiful today, by the way”
“Dan Allah Ni’eema”
Zubawa text ɗin ido tayi jin an buɗe ƙofar ɗakin ta juya ta kalli faɗila da ta shigo tana yatsine fuska
“Wai kam lafiyarki ina Na’ima? Is something wrong with u ne? Tun da kika dawo ɗazu nake tambayarki kince ba komai kuma har yanzu u look moody”
“Miƙewa tayi tana ƙaƙalo murmushi “babu komai fa anty faɗeela stress ne kawai na makaranta”
“Okay amma…” cije bakinta tayi ta gagara ƙarasawa
Da sauri Na’ima ta ƙaraso wajenta tana riƙe ta, “baki da lafiya ne?”
Faɗila ta ɗanyi murmushi “lafiya ta lau fa, kawai cikina ke ɗan ciwo ba sosai bane amma”
“To ai da kin zauna kin huta”
“Eh kar ki damu zamu je asibiti da baby Gobe its not serious amma dai gwara muje muji miye ne”
“Eh ya kamata”
“Toh tun da kince ba komai ai sai ki fito kici abinci koh? Tunda kika dawo fa baki ci komai ba” faɗila ta faɗa tana nufar ƙofa
“Toh” Na’ima ta faɗa a hankali tana bin faɗeela da kallo, sosai take jinta a ranta kamar uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, ko dan yawan kulawarta gareta, ko dan bata saba da irin wannan bane oho, back in newyork babu wanda ya damu taci abinci ko bata ci ba, ba wanda dan bata fito ba ta wuni a ɗakinta zai damu kamar yadda Faɗeela ke damuwa haka, tayi murmushi ta ɗauki hula ta saka ma kanta da tama 2 braid ta dawo da jelan ta gaba ya sauƙo har chest ɗinta ta nufi ƙofa ta fita.
Ko da dare yayi kasa bacci tayi, ta buɗe text ɗin sadiq tana bi a hankali amma sai ta kasa masa reply, wanda zuwa lokacin ya sake kiranta ba adadi ya tura mata messages da har suka fara bata tsoro, cause gabaɗaya gani take kamar ba sadiq ɗin da ta sani bane wannan. Ƙarshe littafanta ta kwaso da laptop ɗinta da niyyar karatu amma shima ta gagara.
Da ƙyar bacci ya ɗauke ta around 1:30 na dare, ƙarfe biyu cif taji ana ƙwanƙwasa ƙofarta, ta miƙe da sauri tana mutsuka idonta, jin muryar Nasir yana kiran sunanta yasa ta sauƙa daga gadon da sauri tana ture books ɗinta da ke baje akan gadon ta zura hijab ɗin sallarta ta buɗe ƙofar, yadda ta gansa kaɗai ya tabbatar mata ba lafiya, kafin ma ta tambaya taga yayi gaba da sauri, da sauri ta biyo bayansa dan sai lokacin ta lura da jinin da ya ɓata masa kayan baccin jikinsa kaɗan, jikinta har rawa yake take bin bayansa ganin kamar zai tashi sama, ya buɗe ƙofar palourn ya fita da gudu ta bi bayansa dan yadda yake tafiya yafi ƙarfin saurinta, motarsa ya nufa ganin back seat a buɗe ta ƙarasa wajen da sauri tana kallon faɗila dake kwance tana muƙurƙusu tana kiran sunanta bata san sanda ta faɗa motar ba ta rufe motar tana riƙo faɗeelar jikinta da kiran sunanta, tuni Nasir ya tada motar mai gadi da tun fitowarsu na farko ya buɗe gate yana tsaye yana kallonsu cike da tausayi ya ɗaga musu hannu yana faɗin “Allah ya tsare ”ganin yadda Nasir ya figi motar da banzan gudu ya fita a gidan.
Yadda faɗeela ke kuka haka Na’ima ke kuka tana jijjiga faɗeela da jini ke bin ƙafarta yana ɓata kan kujera zuwa ƙasan motar har suka isa babban asibitin da take ganin likita, tuni likitoci suka rufu a kanta son sanin miye matsalar, Na’ima ta zauna a kan kujera tana kallon ƙofar ɗakin da aka shiga da ita tana hawaye, Nasir dake tsaye jingine da bango ya harɗe hannayensa ya dube ta ganin har lokacin kuka take ya sa ya ƙaraso ya zauna a kujera ɗan nesa da ita “she’ll be fyn stop crying” ya faɗa yana kallon ƙasa dan shima da da hali hawayen zaiyi, ta gyaɗa masa kai tana kallonsa “amma me ya same ta?” Ɗago kanshi yayi ya kalleta “ta farka zata je toilet, shine sai ta faɗi then dis..” ya faɗa yana juyar da kansa gefe dan ya riga da ya cire rai sunyi loosing ɗin baby ɗinsu shi yanzu damuwarsa they should save his wife.



